Malami: 'Yan daba sanye da kayan sojoji ne suka yi harbe-harbe a Lekki
- Ministan shari'ar Najeriya kuma antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, ya yi magana a kan harbin Lekki
- Kamar yadda ya bayyana, akwai yuwuwar wasu bata-gari ne suka saka kayan sojoji inda suka yi harbe-harben
- Ya ce akwai bukatar a tsananta bincike domin bankado gaskiyar abinda ya faru a Lekki tollgate
Abubakar Malami, antoni janar na tarayya, ya ce akwai yuwuwar 'yan daba ne suka saka kayan sojoji sannan suka dnga harbe-harbe a Lekki tollgate da ke jihar Legas.
Kusan makonni biyu da suka gabata ne matasa suka fara zanga-zanga inda suka bukaci a kawo karshen zaluncin 'yan sanda a fadin kasar nan.
Tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amshi bukatar inda ya rushe runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makami, The Cable ta wallafa.
Masu zanga-zangar sun hadu a tollgate inda suka kwashe kwanaki 13 kafin daga baya sojoji su saka masu karfi tare da tarwatsa su.
Akwai rahotanni da ke bayyana cewa wasu daga cikin masu zanga-zangar sun sheka lahira bayan ruwan wutar da 'yan sanda suka musu a tollgate a ranar 20 ga watan Oktoban 2020.
Amma kuma har yanzu babu takamaiman yawan jama'ar da suka rasu kuma babu shaidu kwarara na aukuwar lamarin.
A yayin magana da manema labarai a ranar Litinin a Abuja, AGF Malami ya ce ana kan bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin da ya faru a Lekki tollgate.
Malami ya ce akwai wuya a tantance cewa an yi harbin domin kuwa za a iya hayar 'yan daba da za su kawo hargitsi.
"Ba za a iya cire ran cewa 'yan daba bane suka shiga lamarin domin kawo rikici."AGF yace.
KU KARANTA: Uwargidan gwamnan Kebbi ta yi martani mai zafi ga matashin da ya zargesu da nada 'yan uwa kwamishinoni
KU KARANTA: Karuwa ta kai wa magidanci 'yan sanda saboda ya kwace iPhone 11 da ya siya mata
A wani labari na daban, Gwamna Obaseki na jihar Edo ya yi kira ga 'yan sanda da su koma bakin aikinsu. Bayan rikicin da ya barke ta sanadin zanga-zangar EndSARS, 'yan sanda sun bar ayyukansu a fadin jihar, lamarin da ya kawo rashin doka da oda.
A yayin rikicin, an kai wa ofisoshin 'yan sanda hari tare da balle gidajen gyaran hali na Benin da Oko inda aka sako masu zaman gidan har 1,993, The cable ta ruwaito.
Amma kuma yayin kai ziyarar ban girma ga Johnson Kokumon, kwamishinan 'yan sandan jihar a ranar Litinin, Obaseki ya ce gwamnatinsa za ta biya dukkan kudin asibitin 'yan sanda da suka samu rauni.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng