Da duminsa: 'Yan fashi da makami sun rufe wata babbar hanya a Katsina

Da duminsa: 'Yan fashi da makami sun rufe wata babbar hanya a Katsina

- Da misalin karfe 8:30 na daren Talata ne 'yan fashi suka tare hanyar Bakori zuwa Kabomo da ke jihar Katsina

- Bayan isar labarin, DPO na Bakori ya jagoranci 'yan sandan zuwa wurin inda suka fafata da 'yan fashin

- Sakamakon haka, daya daga cikin 'yan fashin ya yar da bindigar tokarsa suka tsere

'Yan fashi da makamai sun tare hanyar Bakori zuwa Kabomo a jihar Katsina, jaridar Katisna Post ta wallafa hakan

A ranar Talata da misalin karfe 8:30 na dare ne 'yan fashin suka tare hanyar Bakori zuwa Kabomo.

DPO din Bakori ya jagoranci 'yan sanda zuwa wurin, inda suka yi musayar wuta da 'yan fashin, wanda sakamakon haka, daya daga cikin 'yan fashin ya yada bindigar tokarsa, wacce 'yan sandan suka dauke.

An cigaba da bincike don damko wadannan shu'uman mutanen, a cewar kakakin rundunar 'yan sandan, SP Gambo Isah.

'Yan fashi da makami tare da 'yan bindiga sun dade suna yadda suke so a jihar Kastina. Sun mayar da hankali wurin sace mutane su boye har sai an bada kudin fansa.

A wasu lokutan idan aka yi rashi sa'a ko kuma lamarin ya tarar da ajali, su kan kashe mutum kafin su karba kudin fansar.

Akwai lokutan da su kan karbe kudin fansar su hada da wanda ya je kai wa ko kuma su karba sannan su kashe mutum inda daga bisani a ke tsintar gawar.

KU KARANTA: Ahmad Bamalli: Kotu ta saka ranar sanar da makomar sabon sarkin Zazzau

Da duminsa: 'Yan fashi da makami sun rufe wata babbar hanya a Katsina
Da duminsa: 'Yan fashi da makami sun rufe wata babbar hanya a Katsina. Hoto daga katsinapost.com.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: EndSARS: Kashe 'yan sanda babban abun Allah wadai ne - El-Rufai

A wani labari na daban, samarin unguwar Daudu da ke karamar hukumar Guma a jihar Benue, sun fara zanga-zangar a ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamba, a kan batan mazakutarsu a cikin kauyen.

Kamar yadda rahotonni suka gabata, samari 7 kenan a kauyen suka duba mazakutarsu suka ga tayi layar zana. Wani matashi ya kashe kansa a ranar 11 ga watan Oktoba, bayan an zargesa da sace mazakutar wani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng