Kalli yadda wannan dan bautar kasar ya nemi auren kyakyawar budurwarsa bayan ya yi suman karya (bidiyo)

Kalli yadda wannan dan bautar kasar ya nemi auren kyakyawar budurwarsa bayan ya yi suman karya (bidiyo)

- Wasu masoya biyu da suka kasance yan bautar kasa sun nuna wa duniya ainahin soyayya ta gaskiya

- Da yake neman auran yarinyar, matashi mai yiwa kasa hidimar ya yi karyan kamuwa da rashin lafiya mai tsanani, lamarin da ya jefa budurwar tasa cikin rudani

- Yayinda kyakyawar budurwar ta shiga rudani, sai saurayin ya ciro zobe sannan ya nemi ta aure shi

A wani lamari da za a iya kira da sabon salon neman aure, wani matashi dan Najeriya ya nemi auran kyakyawar budurwarsa.

Kasancewar masoyan biyu duk masu yiwa kasa hidima ne wato NYSC, saurayin ya yi suman karya inda yayi kamar ya kamu da ciwon ciki mai tsanani.

Mawuyacin halin da yayi karyan shiga ya sa hankalin budurwar nasa tashi inda ta shiga rudani, tana ta ihun nemawa saurayin nata agaji daga mutanen da ke kallonsu.

KU KARANTA KUMA: Mun gode da baku zama ɓarayi irin sauran ba: Buhari ya jinjina wa matasan Borno

Kalli yadda wannan dan bautar kasar ya nemi auren kyakyawar budurwarsa bayan ya yi suman karya (bidion)
Kalli yadda wannan dan bautar kasar ya nemi auren kyakyawar budurwarsa bayan ya yi suman karya Hoto: Yabaleft
Asali: Instagram

Tuni dai bidiyon ya shahara a soshiyal midiya, yayinda wani ya zo da ruwa domin ya yayyafa masa, a take sai saurayin ya fito da zobe daga aljihunsa sannan ya mikawa budurwar.

KU KARANTA KUMA: Bukin Maulud: Muhimman abubuwa 5 da Buhari ya faɗa wa yan Nigeria

Lamarin ya sanya yar bautar kasar cikin shauki yayinda ta rufe bakinta da hanayyenta cike da farin ciki. Mutane na ta ihun cewa ta amsa masa da Eh.

Kalli bidiyon a kasa:

A wani labari na daban, mun ji a baya cewa Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, ya dauki nauyin auren marayu 100 a kananan hukumomin Karasuwa da Nguru, jihar Yobe.

“Mun kasance a nan domin daukar nauyin auren matasa 50 a Nguru da wasu 50 daga karamar hukumar Karasuwa,” in ji Lawan.

Lawan wanda ya samu wakilcin Ahmed Mirwa, kakakin majalisar dokokin jihar Yobe, ya ce anyi shirin ne domin tallafawa matasa wadanda suka isa aure amma basu da karfin yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng