COVID-19: Shugaba Donald Trump ya tambayi Malaman asibiti ko zai mutu

COVID-19: Shugaba Donald Trump ya tambayi Malaman asibiti ko zai mutu

- Ana rade-radin Donald Trump ya tambayi Likitoci ko COVID-19 za ta kashe shi

- Shugaban na Amurka ya na jinyar Coronavirus tare da Matarsa, Melania Trump

- Kwararrun Likitoci da Malaman jinya ne su ke kula da shugaban kasar Amurkan

Jaridar Mirror ta fitar da rahoto a ranar 3 ga watan Oktoba, 2020, game da halin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ke ciki a asibitin sojoji.

Donald Trump ya na kwance a babban asibitin cibiyar sojoji na Walter Reed bayan an tabbatar da cewa shi da mai dakinsa, sun kamu da COVID-19.

Shugaban na Amurka ya tambayi Likitocin da su ke duba sa ko zai yi rai, hakan na zuwa ne bayan cutar COVID-19 ta ga bayan wani abokinsa, Stan Chera.

KU KARANTA: COVID-19: Addu’ar da Shugaba Buhari ya yi wa Trump ta jawo suka

Halin da Donald Trump ya ke ciki ya zama abin ta-cewa inda Dr. Shaun Dooley, ya ce shugaban Amurkan ya na jin kansa garau kamar ya koma gida.

Wasu kuma su na rade-radin sai da aka kakaba wa Trump mai shekaru 74 na’urar numfashi.

Likitan fadar shugaban kasar Amurka, Dr Sean Conley, ya yi gum lokacin da manema labarai su ka nemi jin labarin halin da Donald Trump ya ke ciki.

Sunday Mirror ta ce Trump ya matsa a kan sai mutane sun gan shi ya na tafiya da kafafunsa, a lokacin da Hadimansa ke bada shawarar dora shi a keke.

KU KARANTA: Jerin alkawuran da Trump ya cika da wadanda ya saba a mulki

COVID-19: Shugaba Donald Trump ya tambayi Malaman asibiti ko zai mutu
Donald Trump Hoto: Independent
Asali: UGC

Wani na kusa da shugaban ya ce: “In dai Trump ne, duk don idanun jama’a ne.” Ya ce larurar rashin lafiya na iya kawo masa cikas a yakin neman zaben Amurka.

Yayin da ku ka ji cewa Trump da mai dakinsa watau Melania Trump su na jinya a asibiti, masoyan shugaban sun fito su na yi masa addu’ar samun sauki.

Shugaba Trump ya na fuskantar barazana saboda nauyinsa da kuma yawan shekaru.

A ranar Juma'a, shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana game da halin da Trump ya ke ciki, ya yi shugaban kasan Amurka da uwargidarsa faran samun sauki.

Buhari ya rubuta: "Ina yiwa shugaban kasar Amurka da uwargidarsa, fatan samun lafiya."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel