Majalisar Oyo ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi 13

Majalisar Oyo ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi 13

- Majalisar dokokin jihar Oyo ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi goma sha uku

- An tattaro cewa an dakatar da su ne saboda kin bayar da hadin kai ga wani hukunci da majalisar ta zartar

- Ciyamomin kananan hukumomin Akinyele ta gabas, Ido, Oluyole da Ibadan ta gabas na daga cikin wadanda abun ya shafa

Majalisar dokokin jihar Oyo a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba, ta sanar da dakatar da shugabannin rikon kwarya na kananan hukumomi 13 a fadin jihar.

A cewar jaridar The Nation, an dakatar da su ne har sai baba ta gani saboda kin bin shawarar da majalisar jihar ta yanke.

KU KARANTA KUMA: Shekaruna 95 amma har yanzu inda amfani da shafukan soshiyal midiya – Tanko Yakasai

Majalisar Oyo ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi 13
Majalisar Oyo ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi 13 Hoto: @Adebo_ogund
Asali: Twitter

Kananan hukumomi da abun ya shafa sune karamar hukumar Akinyele ta gabas, karamar hukumar Ido, karamar hukumar Oluyole, karamar hukumar Ibadan ta arewa maso gabas.

Sai karamar hukumar Lagelu ta yamma, karamar hukumar Soro da karamar hukumar Ogbomosho ta tsakiya, karamar hukumar Ogbomosho ta kudu.

KU KARANTA KUMA: Ibrahim Sharukan ya yi zazzafan martani a kan hoton Rahama Sadau, bidiyo

Sauran sune karamar hukumar Ajorosun, karamar hukumar Ibarapa ta arewa maso yamma, karamar hukumar Itesiwaju, karamar hukumar Oyo ta gabas da kuma Oyo ta karamar hukumar Kudu maso gabas.

A wani labari nna daban, mun ji cewa majalisar dattawa ta shake ministan yada labarai, Lai Mohammed a dalilin wata kwangila.

Ma’aikatar yada labarai ta cusa wata kwangila ‘ERPG 10145116’ a kasafin kudin shekarar 2020 wanda gwamnatin tarayya ta dauki nauyin aikin.

Rahoton ya bayyana cewa an ba ma’aikatar yada labarai Naira miliyan 250 domin wannan aiki.

Ministan ya jagoranci sauran manyan ma’aikatarsa a ranar Talara, 3 ga watan Nuwamba, 2020, domin su kare kasafin kudin 2021 a gaban majalisa.

Shugaban kwamitin yada labarai a majalisar dattawa, Sanata Abdullahi Sankara, ya ce su na bin Lai Mohammed bashin bayani game da kwangilar.

Abdullahi Sankara ya ce duk da an biya kudin kwangilar cif, amma babu alamun an kama hanyar kammala wannan aiki na gina tashar NTA a Gashua.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng