Shekaruna 95 amma har yanzu inda amfani da shafukan soshiyal midiya – Tanko Yakasai

Shekaruna 95 amma har yanzu inda amfani da shafukan soshiyal midiya – Tanko Yakasai

- Jigon Arewa, Malam Tanko Yakasai, ya bayyana irin rawar ganin da shafuka sadarwa ke takawa wajen debe masa kewa

- Yakasai ya ce duk da tsufansa hakan baya hana shi amfani da shafin soshiyal midiya da sauran fasahar zamani

- Ya ce ya kan duba labaran duniya da sauransu ta wayarsa sannan ya ce yana yi WhatsApp

Shahararren dan siyasan jumhuriya na farko, Malam Tanko Yakasai, ya bayyana cewa tsufansa bai hana shi amfani da shafin soshiyal midiya da sauran fasahar zanani ba kamar sauran tsararrakinsa.

Tanko Yakasai, wanda aka haifa a shekarar 1925, ya ce yana amfani da wayarsa ta hannu wajen karanta labarai da kuma duba wasu muhimman bayanai da dama.

A wata hira da sashin Hausa na BBC, Yakasai ya ce har yanzu baya amfani da madunin ido wajen yin karatu domin yana gani sosai da idanunsu.

KARANTA: Kotu ta datse igiyar auren shekara 10 bayan mata ta zargi miji da halin bera

Shekaruna 95 amma har yanzu inda amfani da shafukan soshiyal midiya – Tanko Yakasai
Shekaruna 95 amma har yanzu inda amfani da shafukan soshiyal midiya – Tanko Yakasai Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

“Ina karanta lamura da dama game da duniya ba tare da madubin ido ba kuma da wayana nake karatun.

“Wasu lokutan, na kan bude shafin WhatsApp don ganin bayani da kuma karantawa.

“Idan yana da tsawo, sai na huta kadan sannan daga bisani na ci gaba.”

Kan lamarin lafiyarsa, Tanko Yakasai ya ce bai da kowani irin cuta da ke damunsa, inda ya kara da cewa ya yi gadon tsawon rai ne daga iyayensa.

KU KARANTA: IGP Adamu ya nada AIG Dandaura da AIG Adamu Alkali su shugabanci wasu bangare 2 a NPF

“Ina da yan uwa da yawa da ke raye amma duk na fi su yawan shekaru kuma na yi gadon haka ne daga iyayena.

“Haka muke a danginmu. Mahaifina ya rasu yana da shekaru 96, kakana ya rasu yana da shekaru 105. Mahaifiyata ce kadai ta rasu tana da shekaru 87. Haka Allah ya yi mu.”

Da yake tuna gwagwarmayar da ya sha, Yakasai ya bayyana cewa an kama shi sau 10 a lokacin mulkin mallaka.

“Ni a siyasata an kama ni sau 10, imma a kama ni a kai ni gaban alkali a daure ko a tsare ni a ofishin yan sanda. Hudu a lokacin mulkin Turawa, hudu a lokacin jumhuriyya ta daya sannan biyu a zamanin Buhari da Babangida,” in ji shi.

A wani labarin na Legit.ng Hausa, Firaministan haɗaɗɗiyar daular larabawa, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, ya bayyana cewa an yi masa gwajin allurar rigafin cutar korona wadda jami'an lafiyar UAE suka ƙirƙira.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel