Thiago Alcantara ya harbu da kwayar cutar COVID-19 inji Liverpool

Thiago Alcantara ya harbu da kwayar cutar COVID-19 inji Liverpool

- ‘Dan wasan tsakiyan Liverpool Thiago Alcantara ya kamu da Coronavirus

- Liverpool ta bayyana cewa sabon ‘dan kwallon na ta ya killace kansa yanzu

- Tsohon ‘Dan wasan na Barcelona bai zai samu buga wasansu da Arsenal ba

‘Dan wasan tsakiyar Liverpool, Thiago Alcantara, ya na dauke da kwayar cutar COVID-19. Kungiyar Ingilar ta tabbatar da wannan.

A ranar Talata, 29 ga watan Satumba, 2020, kungiyar Liverpool ta sanar da cewa sabon ‘dan wasanta ya kamu da ciwon Coronavirus.

Thiago Alcantara mai shekara 29 da haihuwa bai samu damar buga wasan Liverpool da Arsenal na ranar Litinin a dalilin wannan cuta ba.

KU KARANTA: Messi yaji haushin saida Suarez zuwa Madrid

Yanzu haka ‘dan wasan da Liverpool ta sayo daga Bayern Munich ya killace kansa kamar dai yadda aka saba domin takaita yaduwar cutar.

Zakarun na firimiya su ka ce: “An gano cewa Thiago Alcantara ya kamu da Covid-19, kuma yanzu haka ya killace kansa kamar yadda aka tanada.”

“Kungiyar ta na bi, kuma za ta cigaba da bin duk wasu ka’idojin Covid-19, sannan Thiago zai cigaba da killace kansa na lokacin da ake bukata.”

Bisa dukkan alamu, a sakamakon jinyar da ya ke yi, ‘dan wasan ba zai buga wasan kofin da Liverpool za ta sake gwabzawa da Arsenal ba.

KU KARANTA: Barcelona ta sallami 'yan wasa 5

Thiago Alcantara ya harbu da kwayar cutar COVID-19 inji Liverpool
Thiago Alcantara Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Haka zalika Thiago Alcantara ba zai buga wasan Liverpool da kungiyar Aston Villa ba, amma ana sa rai zai warke kafin haduwar Merseyside.

A ranar Litinin dinnan aka tabbatar da cewa ‘yan kasa da ma’aikata 10 na kungiyoyin Ingila su ka kamu da COVID-19 a makon da ya wuce.

A baya kun samu labarin yadda Liverpool ta sayi Thiago Alcantara daga kungiyar Bayern Munich da ke kasar Jamus a kan kudi kusan fam miliyan 30.

Thiago mai bugawa tsakiyar Sifen ya shafe tsawon shekaru 7 tare da kungiyar Bayern Munich.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel