Kasar Masar za ta mayar da yan Najeriya 7 gida saboda zanga-zangar EndSARS
- Hukumomi a Masar sun ce za su dawo da wasu 'yan Najeriya gida, sakamakon gudanar da zanga-zangar EndSARS ba tare da neman izini ba
- Shugabar hukumar kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa ce ta tabbatar da hakan
- Mutanen dai sun shiga sahun masu gudanar da zanga-zangar kawo karshen cin zarafin da yan sanda ke yi wa alúmma a ranar 18 ga watan Oktoba
Shugabar hukumar kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, a jiya Litinin, 2 ga watan Nuwamba, ta bayyana cewa za a dawo da bakwai daga cikin yan Najeriya takwas da suka gudanar da zanga-zangar EndSARS a Masar.
A wasu jerin wallafa da tayi a shafin Twitter, Dabiri-Erewa ta ce bayan kamunsu, sun roki hukumar da ta sanya baki sannan ta tabbatar da sakinsu.
“Karin bayani kan yan Najeriya takwas da aka tsare a birnin Cairo saboda yin zanga-zanga ba tare da izini ba: mahukunta a kasar Masar sun ce za a dawo da bakwai daga cikin yan Najeriya takwas da suka gudanar da zanga-zanga a ranar 18 ga watan Oktoba gida Najeriya saboda rashin takardar izinin zama/biza.
“Dan Najeriya daya daga cikinsu wanda keda takardar zama zai kammala tantancewarsa daga ministan cikin gida na Rasa, Mahmoud Tawfik, bayan ya dauki rantsuwar kin sake aikata wani abu ba tare da izinin mahukunta ba yayin kasancewarsa a kasar,” in ji ta.
Idan za a tuna an kama yan Naeriya takwas a Cairo, Masar, kan yin zanga-zanga a kan cin zarafin yan sanda da kashe-kashe a Najeriya.
KU KARANTA KUMA: Kannywood: Babban darakta Falalu dorayi ya yi wa Rahama Sadau shagube a kan shigar da ta yi
KU KARANTA KUMA: Ibrahim Sharukan ya yi zazzafan martani a kan hoton Rahama Sadau, bidiyo
A gefe guda, hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ba za ta tursasa ma kowani jami’in dan sanda komawa bakin aiki ba, jaridar Premium Times ta ruwaito.
Jawabin martani ne ga wata wallafar jarida wacca ta bayyana cewa hukumar ta yi barazanar korar duk jami’an da suka ki dawowa bakin aiki.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng