Kaduna: Gwamna El-Rufai ya karbi bakuncin Gambari, Sarakuna da Jami’an Gwamnati

Kaduna: Gwamna El-Rufai ya karbi bakuncin Gambari, Sarakuna da Jami’an Gwamnati

- Gwamnonin Arewa da Sarakunan yankin sun shiga wani taro a Jihar Kaduna

- Ministoci da ‘Yan Majalisa su na cikin wadanda ake yin wannan zaman da su

- Gwamna Nasir El-Rufai ya karbi bakuncin Ibrahim Gambari, IGP da wasunsu

Gwamnoni 19 na yankin Arewacin Najeriya, tare da manyan Sarakunan kasar sun shiga wani taro tare da hadimin shugaban kasa, Ibrahim Gambari, a Kaduna.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya na cikin wadanda su ke halartar wannan taro da ya ke gudana a gidan gwamnatin Kaduna, Sir Kashim Ibrahim.

Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya tabbatar da wannan zama a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba, 2020, da safe.

KU KARANTA: Boko Haram sun yi ta'adi bayan sakacin jami'an tsaro

Sufetan ‘yan sanda, Mohammed Adamu da Ministocin yada labarai, Lai Mohammed da kuma Ministan birnin tarayya, Mohammed Bello, su na wajen taron.

Sarakunan da su ke halartar wannan zama sun hada da na na Zazzau, Ahmad Bamalli, Sarkin Hadejiya, Adamu Maje, Sarakunan Bauchi da na kasar Nufawa.

Ga abin da gwamnan ya ce a Twitter:

"Malam Nasir @elrufai ya karbi bakuncin kungiyar gwamnonin Najeriya, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, shugaban majalisa da sauran sanatoci, ministoci, IGP, da sarakuna a Kaduna inda su ka zo taro.

KU KARANTA: Wata cuta ta shiga gari, ta hallaka mutane 15

Kaduna: El-Rufai ya karbi bakuncin Gambari, Sarakuna da Jami’an Gwamnati
Gwamnoni a taron Kaduna Hoto: Twitter/GovKaduna
Asali: Twitter

Gwamna El-Rufai ya yi wa manyan jami’an tsaro, jami’an gwamnati da ‘yan majalisa da manyan Arewa barka da zuwa, inda ya yi tsokaci game da halin da ake ciki.

Nasir El-Rufai a jawabinsa wajen taron, ya ce annobar COVID-19 ta taimaka wajen tabarbarewar halin da ake ciki na rashin aikin-yi da wahalar neman na-abinci.

“Jihohin Arewa da-dama su na fuskantar kalubalen rashin tsaro. Tsagerancin miyagu ya jefa kauyuka da birane cikin barazana.” Inji gwamnan na Kaduna.

Dazu kun ji cewa a Enugu, an samu wadanda su ka bankawa Masallatai wuta bayan wasu musulmai sun daba wa wani Direban Keke-Napep wuka a Nsukka.

Sai dai har yanzu Gwamnati ba ta ce uffan ba a game da harin da aka kai a kudancin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel