Obaseki ya roki jami'an 'yan sanda da su koma bakin ayyukansu

Obaseki ya roki jami'an 'yan sanda da su koma bakin ayyukansu

- Godwin Obaseki, Gwamnan jihar Edo ya koka da yadda 'yan sanda suka bar ayyukansu tun bayan rikicin da ya barke

- A makon da ya gabata ne bata-gari suka dinga kone-kone tare da balle gidajen gyaran hali a jihar Edo

- Gwamnan ya dauka alkawarin biyan kudin maganin 'yan sanda da suka samu raunika tare da gyara ababen da suka lalace

Gwamna Obaseki na jihar Edo ya yi kira ga 'yan sanda da su koma bakin aikinsu. Bayan rikicin da ya barke ta sanadin zanga-zangar EndSARS, 'yan sanda sun bar ayyukansu a fadin jihar, lamarin da ya kawo rashin doka da oda.

A yayin rikicin, an kai wa ofisoshin 'yan sanda hari tare da balle gidajen gyaran hali na Benin da Oko inda aka sako masu zaman gidan har 1,993, The cable ta ruwaito.

Amma kuma yayin kai ziyarar ban girma ga Johnson Kokumon, kwamishinan 'yan sandan jihar a ranar Litinin, Obaseki ya ce gwamnatinsa za ta biya dukkan kudin asibitin 'yan sanda da suka samu rauni.

"Gwamnatin jihar Edo za ta fara gina wuraren da aka lalata. Tuni muka bada kudin motocin sintiri kuma muna fatan isowarsu a mako mai zuwa. Za mu biya kudin maganin 'yan sanda da suka samu rauni," yace.

"Za mu kama dukkan dan fursunan da ya tsere. 'Yan daba sun kone wasu wuraren suna tsammanin sun kona bayanan 'yan fursunan, basu sani ba muna da wasu shaidu na daban."

A yayin martani, shugaban 'yan sandan jihar ya ce sun yi nasarar damke masu laifi 126 kuma 10 daga ciki duk daga gidan yarin suke.

Ya kara da cewa, kusan jami'ansu 11 ne suka samu rauni amma an sallama 10 daga asibiti yayin da dayan yake asibitin koyarwa na Benin.

KU KARANTA: Ba na goyon bayan kai wa masu zanga-zanga hari - Buhari ga matasa

Obaseki ya roki jami'an 'yan sanda da su koma bakin ayyukansu
Obaseki ya roki jami'an 'yan sanda da su koma bakin ayyukansu. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: WAEC: Adadin wadanda suka samu nasara da yawan wadanda aka rike wa sakamako

A wani labari na daban, dakarun sojin saman Najeriya basu dauka kiran da aka dinga musu ba domin su kawo dauki ga jama'ar kauyen Takulashi da ke gundumar Shikarkir a karamar hukumar Chibok ta jihar Borno, majiyoyi daga rundunar ta tabbatar wa The Cable.

Wurin karfe 10 na safiyar Lahadi, wasu mayakan ta'addanci sun tsinkayi kauyen inda suka dinga harbe-harbe sannan suka banka wa gidaje wuta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel