Abinda yasa ba mu janye yajin aiki ba - ASUU

Abinda yasa ba mu janye yajin aiki ba - ASUU

- Kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya, ASUU ta ce ba ta janye yakin aikin ta bane don har yanzu gwamnati ba ta yi gwajin tsarin UTAS ba

- UTAS dai tsari ne na biya albashi da malaman suka tsara bayan sun ƙi amince da tsarin IPPIS da gwamnatin ta gabatar

- Malaman sun ce sun gabatarwa dukkan masu ruwa da tsaki kuma da zarar gwamnatin ta nuna da gaske ta ke yi za su janye yajin aikin

Ƙungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya, ASUU, ta ce har yanzu ba ta janye yajin aikin da ta ke yi ba saboda tana jira gwamnati ta yi gwaji kan tsarin biyan albashi na UTAS.

UTAS tsarin biyan albashi ne da ASUU ta ƙirƙira don maye gurbin tsarin gwamnati na IPPIS.

Shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi a wata hira da ya yi da The Punch ya ce akwai bukatar gwamanti ta bawa hukumar NITDA dama yin gwaji kan UTAS.

Abinda yasa ba mu janye yajin aiki ba - ASUU
Abinda yasa ba mu janye yajin aiki ba - ASUU. Hoto daga @MobilePunch
Asali: UGC

"NITDA ce za ta yi gwajin, gwamnati ne za ta bada izinin yi don NITDA hukuma ce a ƙarƙashin gwamnati kuma sai ta samu izini za ta yi gwajin."

DUBA WANNAN: An sace babura 300 da wasu kayayyaki a gidan sanata a Ibadan

Da ya ke amsa tambaya kan cewa ko gwamnati ta amince da UTAS, Ogunyemi ya ce, "Har yanzu muna magana, mun sanar da su matsayar mu, muna tunanin za mu gana wannan makon idan ba su canja tsarinsu ba. An ɗage taron ranar Litinin. Sun amince da UTAS sun kuma ce mu tafi muyi gwaji a bangaren mu mun fara aiki. Mun gabatar wa ɓangarori uku UTAS, ma'aikatar ilimi, shugaban majalisar dattawa da jami'an ma'aikatar kuɗi da ofishin akanta janar inda dukkan masu ruwa da tsaki ciki har da NITDA suka hallarta. Idan gwamnati ta amince da shi ba wani abu da zai ɗauki lokaci bane."

Ogunyemi ya kuma yi bayyani cewa ASUU a shirye ta ke ta koma aiki idan gwamnati ta shirya yin abinda ya kamata.

KU KARANTA: Bidiyo: Ɗan zanga-zanga ya saci wayar ma'aikaciyar jinya da ta kula da shi ya ɓoye cikin ɗan kamfai

"Mambobin mu a shirye suke su koma aiki idan har gwamnati za ta yi abinda ya dace a bangarenta. Ina fata ba ka nufin mambobin mu su koma aiki tare da yunwa a cikinsu or kuma a janye yajin aikin ba tare da wani ƙwaƙwaran mataki daga ɓangaren gwamnati ba. Ba son yajin aikin mu ke yi ba don ɗaliban yaran mu ne."

A bangaren mu, ba mu da matsala kan komawa aiki, amma muna son adalci a bangaren gwamnati.

"A halin yanzu ba mu ga dalilan da zai sa mu yarda cewa gwamnati za ta yi abinda ta ke faɗa mana ba amma da zarar mun ga alamar da gaske su ke yi, za mu fada wa ƴan Najeriya."

A wani labarin, Shugaba Buhari ya amince da nadin Sanata Oladipo Olusoga Odujinrin, MFR, a matsayin shugaban wucin gadi na kwamitin masu bada shawarwari a hukumar kula da yaduwar kanjamau, NACA, na shekaru hudu.

Nadin zai fara aiki daga ranar 6 ga watan Oktoban 2020 kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel