Da duminsa: NECO ta saka ranar cigaba da jarabawa

Da duminsa: NECO ta saka ranar cigaba da jarabawa

- NECO ta bayyana ranar 9 ga watan Nuwamban 2020 a matsayin ranar cigaba da jarabawarta a fadin kasar nan

- Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta dakatar da rubuta jarabawar ne tun bayan da rikicin EndSARS ya barke

- Hukumar ta ce za ta fitar da sabon jadawalin jarabawar nan da ranar Laraba inda za a ga sabon tsarin da za a bi

Hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO) ta ce za a cigaba da rubuta jarabawar masu kammala sakandare na wannan shekarar bayan dage ta da aka yi sakamkon rikicin EndSARS da ya barke a fadin kasar nan

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayyana, mai magana da yawun NECO, Azeez Sani, ya sanar da cewa za a cigaba da jarabawar a ranar 9 ga watan Nuwamba.

Hukumar ta ce wannan cigaban ya biyo baya ne sakamakon sake duba halin da ake ciki bayan dage jarabawar da aka yi.

Ya kara da cewa, za a fitar da sabon tsarin da z a bi daga ranar Laraba.

"Hukumar ta takura a kan dage jarabawar da tayi a ranar 25 ga watan Oktoban 2020 sakamakon matsalar tsaro da aka samu sakamakon zanga-zanga da ta barke a wasu sassan kasar nan," takardar tace.

"Bayan dawowar zaman lafiya a jihohin kasar nan da babban birnin tarayya, za a cigaba da jarabawar daga ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamban 2020 zuwa Asabar 28 ga watan Nuwamban 2020."

Hukumar na mika godiyarta ga jama'a da kuma masu rubuta jarabawar a kan hakuri da fahimtar da suka nuna a cikin wannan lokacin, The Cable ta wallafa.

KU KARANTA: A dawo mana da mazakutarmu: Hotunan fusatattun matasa suna zanga-zanga a Benue

Da duminsa: NECO ta saka ranar cigaba da jarabawa
Da duminsa: NECO ta saka ranar cigaba da jarabawa. Hoto daga @TheCablelifestyle
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ba na goyon bayan kai wa masu zanga-zanga hari - Buhari ga matasa

A wani labari na daban, hukumar shirya jarabawa ta Afrika ta yamma ta saki sakamakon jarabawar daliban da suka kammala babbar makarantar sakandare a wannan shekarar.

Shugaban hukumar reshen Najeriya, Patrick Areeghan ya sanar da hakan a ranar Litinin a garin Legas, Premium Times ta wallafa.

Kamar yadda yace, dalibai 1,003,668 da ke wakiltar kashi 65.24 na dukkan daliban da suka rubuta jarabawar sun samu sakamako mai kyau a darussa biyar da suka hada da darasin Turanci da Lissafi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel