WAEC: Adadin wadanda suka samu nasara da yawan wadanda aka rike wa sakamako

WAEC: Adadin wadanda suka samu nasara da yawan wadanda aka rike wa sakamako

- Hukumar WAEC ta sanar da sakin sakamakon jarabawar daliban da suka zauna a wannan shekarar

- Kamar yadda shugaban hukumar na Najeriya ya sanar, kashi 65.24 sun samu nasara har a darussan Lissafi da Turanci

- Ya kara da cewa, kashi 13.98 wanda yayi daidai da dalibai 215,149 ne aka rike wa sakamakonsu

Hukumar shirya jarabawa ta Afrika ta yamma ta saki sakamakon jarabawar daliban da suka kammala babbar makarantar sakandare a wannan shekarar.

Shugaban hukumar reshen Najeriya, Patrick Areeghan ya sanar da hakan a ranar Litinin a garin Legas, Premium Times ta wallafa.

Kamar yadda yace, dalibai 1,003,668 da ke wakiltar kashi 65.24 na dukkan daliban da suka rubuta jarabawar sun samu sakamako mai kyau a darussa biyar da suka hada da darasin Turanci da Lissafi.

Ya ce dalibai 1,338,348 da suka rubuta jarabawar wanda suke wakiltar kashi 86.99 na jimillar daliban sun samu nasara a a kalla darussa biyar.

Patrick Areghan ya sanar da cewa, hukumar ta rike sakamako 215,149 na daliban da suka rubuta jarabawar a wannan shekarar.

Kamar yadda yace, sakamakon da aka rike na wakiltar kashi 13.98 na jimillar wadanda aka saki. Ammaa halin yanzu ana binciken sakamakon wadanda ake zargi da satar jarabawa.

Ya ce dalibai 1,549,740 ne suka yi rijistar jarabawar a wannan shekarar, The Cable ta ruwaito.

"Ana binciken lamarin da kuma rahotannin da aka gabatar wa da kwamitin binciken. Kwamitin za su sanar da hukuncinsu ga daliban da ya shafa ta hannun makarantunsu," yace.

KU KARANTA: Ba za mu sadaukar da rayukanmu a kan ku ba, ku kare kanku - DPO ga 'yan Najeriya

WAEC: Adadin wadanda suka samu nasara da yawan wadanda aka rike wa sakamako
WAEC: Adadin wadanda suka samu nasara da yawan wadanda aka rike wa sakamako. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Kada ku ji tsoro, ku fito mu tattauna - Buhari ga matasa

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya zargi wasu 'yan adawa da daukar nauyin 'yan ta'adda da bata-gari wurin kawo cikas a mulkinsa.

Fintiri yayi wannan zargin ne cikin ranakun karshen mako yayin da yake duba wasu ayyukansa a Yola, babban birnin jihar, Daily Nigerrian ta wallafa.

A cewarsa: "Bai dace ana daukar nauyin bata-gari ba don lalata kayan gwamnati, kamata yayi su zo su ga yadda muke amfani da dukiyar gwamnati wurin yi wa jama'a ayyuka."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel