Ba na goyon bayan kai wa masu zanga-zanga hari - Buhari ga matasa
- Don na bari an yi zanga-zanga ba alamar gazawa ta bace, sai dai dama ce na bada don mutane su bayyana damuwarsu, cewar shugaba Buhari
- Ya kara da cewa babu dalilin da zai sa wani jami'in tsaro ya kai hari ga wani mai tafiya a bakin titi ko kuma zanga-zangar lumana
- Shugaba Muhammadu Buhari ya fadi hakan ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamba a Abuja, yayin murnar zagayowar ranar matasa ta kasa
A ranar Lahadi, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna takaicinsa game da harin da jami'an tsaro suka kai wa masu zanga-zangar lumana a jihohin Najeriya.
Wannan furucin na shugaban kasa ya biyo bayan labaran da suka yi ta yawo a sati biyu da suka gabata, inda ya nuna fushinsa a kan harin da jami'an tsaro suka kai wa masu zanga-zangar lumana na EndSARS.
A watan da ya gabata ne jami'an tsaro suka kai hari ga masu zanga-zangar lumana a jihohin Najeriya kamar Legas, Abuja, Oyo da Delta, Premium times ta ruwaito.
KU KARANTA: 'Yan adawa ke daukar nauyin 'yan daba domin lalata mulkina - Gwamnan PDP ya koka
Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnatin tarayya da ta rushe rundunar SARS. Al'amarin da yafi firgitarwa shine harbe-harben da sojoji suka yi a Lekki toll gate, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 2 sannan mutane da dama sun samu munanan raunuka.
Yanzu haka, gwamnatin jihar Legas ta kafa wata kungiya da za ta yi bincike a kan harbin da aka yi a Lekki.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ne ya sanar da hakan.
A cewar Shehu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wannan maganar ne a ranar Lahadi a Abuja, yayin shagalin zagayowar ranar matasa ta kasa.
KU KARANTA: Dalilin da yasa ba za mu bayyana suna sojin da suka yi kisan Lekki ba - Rundunar soji
Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin ministan Abuja, Muhammad Bello yace, "Babu wani wanda yake bin doka, koda mai jiran mota ne a bakin titi, ko kuma mai zanga-zangar lumana da ya kamata wani jami'in tsaro ya cutar ko kuma ya ci zarafinsa.
"Saboda amincewa ta da jajircewa a kan kare hakkin bil'adama ne yasa na rushe rundunar SARS, kuma har yanzu zan cigaba da ganin na gyara tsarin yadda jami'an tsaro suke gudanar da ayyukansu don mutane su ji dadin rayuwa."
"Don na bari an yi zanga-zanga, ba alama bace ta gazawa ta. Alama ce ta amincewa da siyasa da kuma ba wa mutane damar magana don a yi gyara a wata baraka da suka gani," a cewar shugaban kasan.
A wani labari na daban, a jiya da daddare ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki matasa a Abuja, da su daina zanga-zanga a tituna, su yi kokarin tattaunawa mai amfani da gwamnati, wacce aka shirya musamman don gyara a kan dakatar da zalincin da 'yan sanda ke yi wa 'yan Najeriya.
Shugaba Buhari ya nuna rashin amincewarsa da amfani da karfi da matasa ke yi wurin tayar da tarzoma ga 'yan Najeriya da ba su ji ba ba su kuma gani ba, Vanguard ta wallafa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng