Buhari ya yi alhinin rasuwar babban malami Imam Abduljalil Dabo

Buhari ya yi alhinin rasuwar babban malami Imam Abduljalil Dabo

- Allah ya yi wa Imam Abduljalil Dabo, shugaban cibiyar Musulunci ta Uthman Bin Affan, rasuwa

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi alhini tare da mika sakon ta'aziyyar rasuwa babban malamin

- A cewar Garba Shehu, shugaba Buhari ya bayyana marigayi Imam Dabo a matsayin wanda ba ya tsoron fadar gaskiya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi alhini tare da mika sakon ta'aziyyar rasuwar babban limamin cibiyar Musulunci ta Uthman Bin Affan da ke Abuja.

A wani jawabi da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar, Buhari ya bayyana marigayi Dabo a matsayin malami mai karfin gwuiwa, marar tsoro, wanda ba ya tsoron fadawa masu mulki gaskiya a kowanne lokaci.

"Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, ya shiga sahun dubban Musulman Abuja, wajen nuna alhinin rasuwar Imam Abduljalil Dabo, babban limamin cibiyar addinin Musulunci ta Uthman Bin Affan wacce ke kallon ginin Bannex/Emab Plaza a wuse 2, Abuja.

"A cikin sakon da ya aikawa iyali da magoya bayan babban malamin, shugaba Buhari, wanda Dakta Isa Ali Pantami, ministan sadarwa, ya bayyana marigayi Imam Dabo a matsayin jagora nagari, mai karfin halin fadawa shugabannin da ke kan mulki gaskiya," kamar yadda Garba Shehu ya sanar.

KARANTA: 2020: Yadda za a duba sakamakon jarrabar WAEC cikin sauki ta hanyar bin matakai 7

Da ya ke maimaita kalaman Buhari a cikin jawabinsa, Garba Shehu ya ce; "mazauna birnin tarayya (FCT), Abuja, sun rashin babban malami, jagora nagari; mai karfin hali, da kyawawan halaye. Mu na rokon Allah ya karbi kyawawan aiyukansa.

Buhari ya yi alhinin rasuwar babban malami Imam Abduljalil Dabo
Buhari ya yi alhinin rasuwar babban malami Imam Abduljalil Dabo
Asali: UGC

Imam Dabo ya rasu da misalin karfe hudu na yammacin ranar Lahadi bayan ya sha fama da rashin lafiya.

KARANTA: 'Yan Najeriya 9 da za'a fafata dasu a zaben kasar Amurka

An yi jana'izarsa da misalin karfe 1:30 na ranar Litinin a masallacinsa da aka fi kira ''Banex Mosque'' da ke Wuse II a Abuja.

Huseyn Zakaria, mai gabatar da tafsiri a Masallacin Bannex, ya ce za a binne gawar marigayi Imam Dabo a makabartar Gudu da ke Abuja.

Marigayi Imam Dabo ya rasu ya bar mata uku da 'ya'ya da jikoki masu yawa.

A ranar Lahadi ne Legit.ng ta wallafa labarin rasuwar tsohon dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar National Action Council (NAC), Cif Olapade Agoro, wanda ya rasu yana da shekaru 77 a duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng