An tura tawagar soji na mata zalla zuwa Anambra (hotuna)

An tura tawagar soji na mata zalla zuwa Anambra (hotuna)

- An tura rundunar sojoji na musamman zuwa jihar Anambra domin tabbatar da zaman lafiya

- Tawagar wadanda suka samu tarba daga gwamnan jihar, Willie Obiano sun kasance mata zalla

- Hakan na zuwa ne bayan an yi fama da rikice-rikice a yankuna da dama na kasar sakamakon zanga-zangar EndSARS

Rundunar sojojin Najeriya ta tura tawagar mata zalla zuwa jihar Anambra domin aikin kiyaye zaman lafiya.

Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya tabbatar da wannan ci gaban a wani wallafa da yayi a shafin Twitter, inda ya kara da cewar an turo rundunar ta musamman domin tabbatar da tsaron mazauna jihar.

KU KARANTA KUMA: Tsohon dan takarar shugaban kasa, Olapade Agoro, ya rasu

An tura tawagar soji na mata zalla zuwa Anambra (hotuna)
An tura tawagar soji na mata zalla zuwa Anambra hoto: @WillieMObiano
Asali: Twitter

“A safiyar yau, na tarbi wata tawagar rundunar soji na musamman da aka turo jiharmu domin taimakawa wajen tabbatar da dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Anambra.

“A kullu yaumin muna ba tsaron rayuka da dukiyoyin mutanen Anambra muhimmanci sannan mun jajirce don daukar dukkanin matakan da suka kamata don tabbatar da kowani dan Anambra ya samu zaman lafiya. Ya yi rasuwa da aiki ba tare da tsoro ba.”

KU KARANTA KUMA: Shugabancin 2023: Ba za mu iya cewa ga yankin da magajin Buhari zai fito ba, Buni

A yan makonnin da suka gabata, zanga-zangar EndSARS wanda ya fara cikin lumana, ya zama hargitsi a yankuna daban-daban na kasar yayinda aka yi sace-sace da lalata dukiyoyin gwamnati da na wasu daidaikun mutane.

Gwamnatin jihar Anambra ta takaita zirga-zirga a kokarin da take na hana yaduwar rikici, amma dai yanzu an sassauta dokar kullen, jaridar The Cable ta ruwaito.

A cewar Obiano, “tawagar ta musamman za ta ci gaba daga inda hazikan jami’an sauran hukumomin tsaro suka tsaya wandan kokarinsu ne ya sa jiharmu ta zamo mafi tsaro a Najeriya.”

A wani labarin, ukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ba za ta tursasa ma kowani jami’in dan sanda komawa bakin aiki ba.

Hukumar PSC din ta bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamba, a cikin wata sanarwa daga Shugaban harkokin labaranta da hulda da jama’a, Ikechukwu Ani.

Jawabin martani ne ga wata wallafar jarida wacca ta bayyana cewa hukumar ta yi barazanar korar duk jami’an da suka ki dawowa bakin aiki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel