Kwamiti ya gano an dankara ayyukan lantarki a cikin karamar hukumar Lau

Kwamiti ya gano an dankara ayyukan lantarki a cikin karamar hukumar Lau

- Ma’aikatar REA ta kare kasafin kudinta na shekara mai zuwa a Majalisa

- An fahimci duk an tattara mafi yawan ayyukan Ma’aikatar a garin Lau

- Ministan wutar lantarki, Sale Mamman, ya fito daga karamar hukumar

A ranar Laraba, 28 ga watan Oktoba, 2020, majalisar dattawa ta yi tir da cusa kwangilolin wuta rututu da aka yi a karamar hukumar Lau, inda Minista ya fito.

Jaridar Punch ta ce ‘yan majalisar dattawan sun gano akalla kwangilolin aikin wutar lantarki 20 da aka ware za a yi a garin Lau da ke jihar Taraba a kasafin 2021.

Kwamitin harkar wuta a majalisar dattawa ta fahimci haka a lokacin da ta ke aiki a kan bangaren ayyukan da ma’aikatar REA za su yi a kasafin shekara mai zuwa.

KU KARANTA: An dakatar da karin kudin shan wutar lantarki - Minista

‘Yan wannan kwamitin sun gano cewa an ware wa garin Lau, mahaifar Ministan wuta, Saleh Mamman, ayyukan da kudinsu ya tashi daga N20m zuwa N52m.

Sanatocin sun yi tir da yadda aka kasafta wadannan ayyuka ganin yadda kwangilar wuta guda rak aka kai wa gaba daya yankin Kudu maso Kudu, a jihar Delta.

Shugaban ma’aikatar REA, Ahmad Salijo, ya tsaya gaban Kwamitin Sanata Gabriel Suswam, ya kare kasafin kudin da su ka gabatar na shekarar 2021 mai zuwa.

Ana cikin wannan zama ne sai Sanatan Taraba, Yusuf Yusuf, ya gano rashin daidaito a kason, ya jawo hankalin abokan aikinsa a kan yadda aka ware kwangilolin.

KU KARANTA: Buratai: Kowane Jami'i sai ya bayyana abin da ya mallaka

Kwamiti ya gano an dankara ayyukan lantarki a cikin karamar hukumar Lau
Ministan wutan lantarki Hoto: www.infoguideafrica.com/2020/08/saleh-mamman-biography.html
Asali: UGC

Ya ce: “Ba batun N52m ba ne, idan ku ka lura daga na 85, N30m, N20m, N40m da sauransu duka, za ku ga cewa duk an dankara su ne a karamar hukuma daya.”

“Nan ne karamar hukumar Minista (Saleh Mamman). Kwangiloli 20 a garin Lau. Ba kalubalantarsa na ke yi ba, na tabbatar da wannan.” Inji Sanata Yusuf.

Kwanakin baya kun ji cewa Tsohon Sarkin Kano da bankin CBN, Muhammadu Sanusi II ya ce cire tallafin man fetur da karin kudin wuta abu ne mai matukar kyau.

Sanusi ya ce nan gaba, mutanen Najeriya za su ga amfanin wannan mataki da aka dauka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel