Rundunar soji ta halaka 'yan bindiga 5, ta rasa soja daya a Katsina
- Sojojin Najeriya sun samu nasarar ceto wasu mata masu goyo 3 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Faskari, jihar Katsina
- Mukaddashin kakakin rundunar sojin, birgediya janar Benard Onyeuko, ya sanar da hakan a wata takarda da ya saki a ranar Lahadi
- A cewarsa, garin gumurzun, sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda 5, sai dai soja daya ya rasa ransa garin ceto daya daga cikin matan
Hukumar sojojin Najeriya ta ce rundunar OSS, da aka samar don kawar da ta'addanci da garkuwa da mutane a arewa maso yamma, ta samu nasarar kashe 'yan ta'adda 5.
Sai dai sun rasa soja daya sakamakon bata - kashin da suka yi da 'yan ta'addan a kauyen Diskiru da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.
Mukaddashin kakakin rundunar, Birgediya Janar Benerd Onyeuko, ya sanar da hakan a wata takarda daya bai wa manema labarai ranar Lahadi a sansanin sojoji da ke Faskari.
Ya ce sun kashe 'yan ta'adda 3 take-yanke, daga baya kuma aka gano gawawwakin 'yan ta'addan guda biyu, Thisday ta ruwaito.
A takardar Onyeuko ya bayyana yadda suka yi gumurzu da 'yan ta'addan har suka samu nasarar ceton wasu mata 3 masu goyo.
Sai dai kash, garin turnukun, sun rasa soja daya yayin da ya ke kokarin ceto daya daga cikin matan.
A cewarsa: "A ranar 29 ga watan Oktoba 2020, rundunar sun mayar da harin da 'yan ta'addan suka kai wa kauyen Diskuru da ke karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina."
KU KARANTA: Tsohon manomi ya datse mazakutarsa saboda zarginsa da gamsar da matan kauyensu
KU KARANTA: Wurin wawushe tallafin korona, dattaijuwa ta rasa ranta a Kaduna
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ce duk wanda ya san ya saci kayan tallafin COVID-19, yayi gaggawar mayarwa cikin awanni 12.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Talata, yayin gabatar da jawabi ga jama'an jihar Adamawa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng