Za mu rushe gidajenku ko mu kwace takardunsu - Gwamna Fintiri ga masu satar tallafi
- Gwamna Fintiri, na jihar Adamawa, ya umarci wadanda suka kwashi kayan tallafin COVID-19 da su dawo dasu cikin awanni 12
- Ya ce matsawar aka kama wani da kayan tagomashin, to tabbas zai sa a rusa masa gidansa, idan kunne ya ji, gangar jiki ya tsira
- Gwamnan ya sanar da wannan kudirin nasa a ranar Talata, yayin gabatar wa da al'ummar jiharsa jawabi cikin fushi
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ce duk wanda ya san ya saci kayan tallafin COVID-19, yayi gaggawar mayarwa cikin awanni 12.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Talata, yayin gabatar da jawabi ga jama'an jihar Adamawa.
KU KARANTA: Ana tsaka da rabon tallafin korona, 'yan daba suka buga wawaso
A cewarsa, "Na bai wa duk wadanda suka saci kayan abinci daga ma'adanar gwamnati daga karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe, su yi gaggawar mayar da kayan abincin ga ofishin 'yan sanda mafi kusa da su."
KU KARANTA: An sace babban basarake har fadarsa a kan rikicin sarauta na shekaru 27
Ya kara da cewa, "Na bayar da wa'adin nan ne don ayi gaggawar bin umarnin gwamnati, don zan tura jami'an tsaro gida-gida su yi bincike karfe 7:00 na safiya."
Ya ce matsawar aka kama wani da kayan satar, to tabbas zai sa a rushe gidansa ko kuma a kwace shedar mallakar gidan. Ya kuma umarci saka dokar hana fita, don dakatar da bata-gari daga cigaba da asara dukiyoyin gwamnati da na al'umma.
A wani labari na daban, daruruwan matasa a ranar Litinin sun yi watsi da dokar ta-bacin da aka saka a Jalingo, sun kutsa tare da tarwatsa kayayyakin aiki na gidan rediyon jihar.
Kwamishinan yada labarai da wayar da kai na jihar, Danjuma Adamu, wanda ya ziyarci gidan rediyon jihar, ya duba farfajiyar tare da ganin irin barnar da aka yi da kuma kushe lamarin.
Kwamishinan ya ce wannan barnar ta zarce zanga-zangar kawo karshen SARS da matasan suka fake da yi, Vanguard ta ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng