Wurin wawushe tallafin korona, dattaijuwa ta rasa ranta a Kaduna

Wurin wawushe tallafin korona, dattaijuwa ta rasa ranta a Kaduna

- Wata mata mai shekaru a kalla 45 ta rasa ranta wurin damben kwaso kayan tallafin COVID-19

- Al'amarin ya faru ne a karamar hukumar Kaura da ke Kagoro a ranar Litinin da misalin karfe 7pm

- Kamar yadda bayanai suka zo, duk da harbe-harben jami'an tsaro da na 'yan sa kai, sai da bata-gari suka kwashe kayan tas

Wata mata ta rasa ranta a daren Litinin yayin damben kwasar kayan tallafin COVID-19 a ma'ajiyar karamar hukumar Kaura dake Kagoro, Daily Trust ta wallafa haka.

Daily Trust sun bayyana yadda mamaciyar, Esther Mba, wacce take da shekaru a kalla 45 ta rasa ranta sakamakon damben dibar kayan tallafin.

Kamar yadda bayanai suka zo, bata-garin sun fara kwasar kayan abincin ne da misalin karfe 7 na daren Litinin, duk da harbe-harben jami'an tsaro da na 'yan sa kai, amma abin ya ci tura.

Kamar yadda sakataren karamar hukumar, Sunday Tibishi, ya shaida, babu wanda jami'an tsaro suka damka.

KU KARANTA: Cire kudi da nayi a asusun bankinka babu izininka hakkina ne - Budurwa ga saurayi

Wurin wawushe tallafin korona, dattaijuwa ta rasa ranta a Kaduna
Wurin wawushe tallafin korona, dattaijuwa ta rasa ranta a Kaduna. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shari'ar nadin Sarkin Zazzau, artabun da aka yi a kotu tsakanin Iyan Zazzau da sauran wadanda ake kara

A wani labari na daban, Ministan ma'aikatan tallafi da jin kan 'yan kasa, Sadiya Umar Farooq ta ce ta yafe wa duk wadanda suka zargeta da boye tallafin rage radadin korona wanda aka ware domin talakawan Najeriya.

Ta sanar da hakan ne yayin amsa tambayoyin manema labarai a Gusau a ranar Litinin da ta gabata, Vanguard ta ruwaito.

"Ina sane da irin zargina da zagi da jama'a ke yi tare da ma'aikatata a kan kayan rage radadi da gwamnatin tarayya ta bayar.

"Ina yawan sanar da cewa ina kokarin sauke nauyin da ke kaina iyakacin iyawata a kuma dukkan sassan kasar nan.

"A yanzu da jama'a suka gane laifinsu da kuskurensu, zan iya addu'ar Allah ya yafe mana baki daya," tace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng