Ba mu da mafita - El-Rufai ya jaddada bukatar gyaran Najeriya

Ba mu da mafita - El-Rufai ya jaddada bukatar gyaran Najeriya

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai, ya ce ya kamata a yi gyara a kan tsarin kundin mulkin Najeriya

- A cewarsa, yakamata jihohi su amfana da ma'adanai da sauran harkokin samun kudin shiga na jihohinsu

- Yayi wannan maganar ne a taron murnar cikar Arewa House shekaru 50, wanda aka yi a Kaduna ranar Asabar

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce lokacin gyara Najeriya ya yi, don raba kayan amfani ga kowanne bangare yadda ya dace da yayi.

Ya fadi hakan ne a wani taron murnan cikar Arewa House shekaru 50, wanda aka yi a Kaduna ranar Asabar. Ya ce gyara tsarin kasar nan shine abu mafi dacewa don kawo cigaba mai dorewa a Najeriya.

El-Rufai, ya lura da yanayin tsarin da kwamitin APC ta samar a 2018 a kan bukatar canja salon kundin mulkin Najeriya wurin bai wa wasu jihohi damar amfani da wasu ma'adanan cikinsu.

Manufar kwamitin APC, wacce El-Rufai ya jagoranta a 2017, ita ce tabbatar da kowanne dan Najeriya ya more a matsayinsa na dan kasa.

A cewarsa, ta haka ne kadai jihohi za su samu damar amfana daga 'yan sanda, man fetur, ma'adanai, rijistar sunayen kamfanoni da sauran harkokin samun kudade.

"Ban san wani kundin tsarin mulki da ya ci karo da bai wa jihohi damar amfana da ma'adanai ba. Wannan zai samar wa jihohi kudaden shiga, ta yadda ba sai sun damu shugaban kasa da gwamnatin tarayya ba idan suna da wasu bukatu," a cewarsa.

KU KARANTA: Tsohon manomi ya datse mazakutarsa saboda zarginsa da gamsar da matan kauyensu

Ba mu da mafita - El-Rufai ya jaddada bukatar gyaran Najeriya
Ba mu da mafita - El-Rufai ya jaddada bukatar gyaran Najeriya. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Binciken gida-gida: Shehu Sani ya yi martani mai zafi ga gwamnati

"Don haka lokaci yayi da za'a canja salon ayyuka, don 'yan kasa su amfana.

"Don haka, kamar yadda kwamitin da APC ta shirya, don samar da dama ga jihohi wurin amfana da harkokin arziki.

"Ina kira ga 'yan majasar tarayya da kuma masu ruwa da tsaki a majalisar dattawa da su yi amfani da wannan rahoton don samar da wannan tsarin mulkin, da kuma gyara nan ba da jimawa ba.

"Za mu yi amfani da wannan damar don samar da cigaba ga kasar mu da mutanenmu. Samar da tsari, dokoki da kuma shirin kundin tsarin mulki na hannunmu don gyara mulkin karni na 21 a kasarmu." yace.

A wani labari na daban, hawaye sun kubce wa Goddy Jeddy Agba, karamin ministan wutar lantarki, a ranar Talata, 27 ga watan OKtoba, yayin da yake zagayen duba asarorin da matasa suka tafka wa Calabar, babban birnin jihar Cross River.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, Agba ya fashe da kuka, bayan ganin irin aika-aikar da bata-gari suka yi a asibitin masu tabin hankali, inda suka lalata tsadaddun abubuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel