Ministan Buhari ya fashe da kuka bayan ya duba barnar da matasa suka yi a jiharsa
- A Calabar, jihar Cross River, matasa sun lalata dukiyoyin gwamnati da dama da ke jihar
- Wannan al'amarin ya sa karamin ministan wutar lantarki, Goddy Agba, zubar da hawaye
- Inda yayi kira ga matasa da su ajiye makamansu, za a yi duk abubuwan da suke so
Hawaye sun kubce wa Goddy Jeddy Agba, karamin ministan wutar lantarki, a ranar Talata, 27 ga watan OKtoba, yayin da yake zagayen duba asarorin da matasa suka tafka wa Calabar, babban birnin jihar Cross River.
Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, Agba ya fashe da kuka, bayan ganin irin aika-aikar da bata-gari suka yi a asibitin masu tabin hankali, inda suka lalata tsadaddun abubuwa.
Gwamna Ayade, ya bayyana irin dumbin dukiyar da jihar Cross River ke bukata don gyara duk abubuwan da aka bata.
KU KARANTA: Ana tsaka da rabon tallafin korona, 'yan daba suka buga wawaso
Ministan ya duba ofisoshin gidan talabijin na NTA, na WAEC da sauran wurare.
Ya bai wa matasa hakuri a madadin gwamnatin tarayya, inda yace ya fahimci irin radadin da suke ji, kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari zai duba bukatunsu.
A cewarsa, "Na yi matukar mamakin irin asarar da muka tafka, daga dukiyoyin har matasan duk namu ne, wajibi ne mu taru mu gyara. Muna bai wa matasa hakuri a kan radadin da suka ji da har ya kai su ga lalata wadannan dukiyoyin, mun fahimcesu kuma za mu gyara."
KU KARANTA: An sace babban basarake har fadarsa a kan rikicin sarauta na shekaru 27
A wani labari na daban, daruruwan matasa a ranar Litinin sun yi watsi da dokar ta-bacin da aka saka a Jalingo, sun kutsa tare da tarwatsa kayayyakin aiki na gidan rediyon jihar.
Kwamishinan yada labarai da wayar da kai na jihar, Danjuma Adamu, wanda ya ziyarci gidan rediyon jihar, ya duba farfajiyar tare da ganin irin barnar da aka yi da kuma kushe lamarin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng