Gwamnati ta lissafa muhimman wurare 22 da mabarnata suka lalata

Gwamnati ta lissafa muhimman wurare 22 da mabarnata suka lalata

- Har yanzu ana cigaba da samun sabbin rahotannin tafka ta'annati da mabarnata ke yi a sassan Nigeria

- Mabarnata na cigaba da kai farmaki wurare daban-daban mallakar gwamnati da daidaikun mutane

- Gwamnatin jihar Filato ta bayyana cewa muhimman wurare 22 mabarnata suka lalata a 'yan kwanakin baya bayan nan

Gwamnatin jihar Filato ta bayyana cewa muhimman wurare 22 mabarnata suka lalata a ta'adin da batagari ke cigaba da yi a sassan Nigeria.

Batagarin matasa sun fake da zanga-zangar ENDSARS wajen fara balle wuraren ajiyar kayayyaki mallakar gwamnati da daidaikun mutane da kuma shiga gidajen manyan 'yan siyasa tare da yin awon gaba da duk kayayyakin da ke ciki.

Ana zargin cewa wasu batagarin matasa sun kwace iko da zanga-zangar ENDSARS domin tafka barna da sauran miyagun laifuka.

Mabarnatan matasa sun tafka barna a mafi yawan manyan shagunan ajiye kayan abinci mallakar gwamnati da daidaikun jama'a da ke sassa daban-daban na Najeriya.

Matasan da ke tafka wannan barna suna kwashe dukkan kayayyakin da suka samu a irin wadannan manyan shaguna.

A yayin da matasan ke ikirarin cewa suna kwashe kayan abincin da gwamnati ta bayar da sunan tallafin korona, rahotanni sun wallafa yadda mabarnatan ke kwasar duk abinda hannunsu ya taba, koda ba mai amfani garesu ba.

KARANTA: Abuja-Kaduna: Masu garkuwa sun kashe Kanal a rundunar soji bayan karbar kudin fansa N10m

A cewar wata sanarwa da gwamnatin jihar Filato ta fitar ranar Talata, ta bayyana cewa wurare 22 mabarnta suka lalata ta hanyar konawa ko kuma ragargazasu.

Gwamnan jihar Filato tare da mambobin majalisar wakilai ta tarayya sun ziyarci ginin 'JIB Complex', gidan tsohon shugaban majalisa, Yakubu Dogara, da kuma ofishin hukumar gyara hanyoyi ta jihar Filato da mabarnata suka lalata.

Gwamnati ta lissafa muhimman wurare 22 da mabarnata suka lalata
Gwamna Simon Lalong
Asali: Twitter

Macham Machut, kakakin gwamna Lalong ya ce; "mambobin majalisar wakilai tare da gwamna Lalong sun ziyarci wuraren da mabarnata suka lalata a Jos da Bukuru a 'yan kwanakin baya bayan nan. Ba mu ji dadin abinda ya faru ba".

Ya ce rikicin ya mayar da jihar Filato baya tare da dora mata nauyin gyara wuraren da mabarnata suka lalata a jihar.

KARANTA: Wanda ya ci ya amayar: Gwamnatin Kaduna ta fara bi gida gida neman kayan tallafin korona da aka wawashe

A cewar Mista Machut, gwamna Lalon ya bukaci jama'a suke kare gine-ginen gwamnati da ke makwabataka da su, ya ce yin hakan zai karawa gwamnati karfin guiwa wajen cigaba da shimfida aiyukan raya kasa.

Yanzu haka jami'an tsaro na cigaba da kama wasu daga cikin mabarnatan matasan tare da kwace kayayyakin da suka kwasa.

Rundunar 'yan sanda ta ce za ta gurfanar da dukkan mabarnatan da ta kama a gaban kotu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel