Ba zai ƙara komai a tattalin arziƙi ba - Ndume ya magantu kan rage albashin ƴan majalisu

Ba zai ƙara komai a tattalin arziƙi ba - Ndume ya magantu kan rage albashin ƴan majalisu

- Sanata Ali Ndume ya yi korafi a kan kira da mutane ke yi na a rage albashin yan majalisun tarayya

- Ndume ya ce babu wani tasiri da zabtare albashin yan majalisun zai yi a tattalin arzikin kasar

- Dan majalisar ya ce biliyan N128 kacal aka ware wa majalisun cikin kasafin kudin triliyan N13 na 2021

Sanata Ali Ndume ya soki kira da ake yi na rage albashin mambobin majalisar dokokin tarayya, ya ce a ganinsa albashin yan majalisar bai da kowani tasiri kan tattalin arziki.

“Bai da kowani tasiri a kan tattalin arziki,” In ji Ndume a shirin Channels Television na yammacin ranar Juma’ a, lokacin da aka tambaye shi game da tasiri albashin yan majalisa kan tattalin arzikin kasar.

Dan majalisar mai wakiltan Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya yi bayanin cewa mambobin majalisar dokokin na tarayya sun samu naira biliyan 128 ne kacal a kasafin naira tiriliyan 13 na 2021.

“A wajena, sukar majalisar dokokin tarayya, a soke NASS. Hakan na nufin za a samu ragin naira biliyan 128 amma shin akwai wani banbanci da hakan zai kawo? Saboda wannan abu (kira ga rage albashin mambobin majalisar tarayya) ya yiwa mutane irina da suka fito domin yin aiki, ba wai don azurta kansu ba yawa.”

KU KARANTA KUMA: Jerin manyan ma'aikatu da ɓata garin Filato suka lalata, ciki har da sakatariyar jihar

Ndume ya yi korafin cewa babu wani dan majalisa da ya taba tara kudi saboda ya kasance a majalisar tarayya.

“Babu wani dan majalisa, ku je ku duba tarihi, babu wanda ya zama mai kudi saboda ya taba rike mukamin dan majalisa,” in ji Ndume.

Ba zai ƙara komai a tattalin arziƙi ba - Ndume ya magantu kan rage albashin ƴan majalisu
Ba zai ƙara komai a tattalin arziƙi ba - Ndume ya magantu kan rage albashin ƴan majalisu Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

A cewarsa, tunda ya shiga siyasa a 2003, rayuwarsa bata sauya ba. Ya kuma ce lallai matsalar kasar nan ya kasance tsadar shugabanci a dukkanin matakan gwamnati.

“Na shiga harkar siyasa a 2003. Ku je ku tambayi mutane, rayuwata bata sauya ba. Tsadar gwamnati ne matsalar. Tsadar gwamnati a dukkan matakai harda majalisar dokokin tarayya,” in ji dan majalisar.

“Amma ba zai yiwu a dunga magana a kan tsadar gwamnati ba, sannan a ware majalisar dokokin tarayya ita kadai.”

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Miyetti Allah ta bankaɗo wanda ke ɗaukar nauyin Zanga-zanga

Ya bayyana cewa baya ga albashi, kasafin da aka warewa mambobin majalisar tarayya a ciki ne za a aiwatar da komai da biyan ma’aikata.

“Da kudi ake gudanar da ofishin,” in ji shi.

A wani labarin, kwamitin majalisar wakilai a kan harkokin 'yan sanda ya ce akwai bukatar a biya diyya ga 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a zanga-zangar EndSARS.

An yi zanga-zanga a fadin kasar nan a kan cin zarafi da zaluncin 'yan sanda a fadin kasar nan, lamarin da ya zarta mako daya.

'Yan Najeriya sun bi tituna inda suke bukatar a gyara ayyukan 'yan sanda amma sai zanga-zangar ta koma wani abu daban

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel