Gwamnan Osun ya bai wa masu satar kayan tallafi wa'adi, ya sanar da abinda za su iya fuskanta
- Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola ya umarci masu zanga-zangar EndSARS da su dawo da duk abinda suka sata yayin zanga-zangar
- A ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba ne gwamnan ya umarci bata-garin, inda ya basu kwanaki 3 su mayar da komai da suka dauka
- Ya ce lallai duk wanda bai mayar da abubuwan da ya dauka ba cikin kwanaki uku, zai fuskanci hukunci mai tsanani
Rahotanni sun nuna yadda bata-gari suka saci dukiyoyin gwamnati, ciki har da kayan abincin tallafin COVID-19 a ranar Asabar. An umarci bata-garin wadanda suka yi satar da sunan zanga-zangar EndSARS da su mayar da duk abubuwan da suka sata cikin kwana 3.
Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola ne ya bayar da wannan umarnin a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, yayin da yake zagaye jihar don ganin barnar da suka yi a jiharsa.
Ya ce idan har basu dawo da duk abubuwan da suka sata ba cikin kwana 3, to tabbas zasu fuskanci fushin hukuma.
KU KARANTA: Tallafin Covid-19: An gane mahaifina ba shine matsalar Najeriya ba - Zahra Buhari
Ya ce su mayar da kayan da suka sata zuwa fadar sarki mafi kusa da su, Legit.ng ta wallafa.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun halaka mutum 6 da ake zargin 'yan Boko Haram ne
A wani labari na daban, Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar Imo, ya yi bayani dalla-dalla a kan dalilan da ke hassalar da matasa suna tada hankulan jama'a, asarar dukiya da kuma tayar da zaune tsaye da sunan zanga-zangar EndSARS.
A ranar Juma'a, 23 ga watan Oktoba, yayin da Sanatan, kuma tsohon gwamnan, wanda yanzu haka shine mai wakiltar mazabar Imo ta yamma, ya yi hira da manema labarai a Abuja, inda yace mulkin kama-karya, zalunci, kunci, bala'i da yunwa ne dalilin da ya tunzuro matasa suka mayar da zanga-zangar EndSARS tashin hankali.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng