Shugabanni su farka, mulkin kama-karya ne yake fusata matasa - Okorocha

Shugabanni su farka, mulkin kama-karya ne yake fusata matasa - Okorocha

- Sanata Rochas Okorocha ya ce mulkin kama-karya ne ya janyo zanga-zangar EndSARS a Najeriya

- Tsohon gwamnan kuma jigon jam'iyyar APC ya ce matasa na yin zanga-zangar ne don farkar da shugabanni

- Okorocha ya ce yanayin rayuwa mai cike da almubazzaranci da shugabanni suke yi shine ke kara harzukar da matasan

Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar Imo, ya yi bayani dalla-dalla a kan dalilan da ke hassalar da matasa suna tada hankulan jama'a, asarar dukiya da kuma tayar da zaune tsaye da sunan zanga-zangar EndSARS.

A ranar Juma'a, 23 ga watan Oktoba, yayin da Sanatan, kuma tsohon gwamnan, wanda yanzu haka shine mai wakiltar mazabar Imo ta yamma, ya yi hira da manema labarai a Abuja, inda yace mulkin kama-karya, zalunci, kunci, bala'i da yunwa ne dalilin da ya tunzuro matasa suka mayar da zanga-zangar EndSARS tashin hankali.

Okorocha ya jajanta wa wadanda suka rasa 'yan uwansu, yaransu da masoyansu sakamakon rikicin.

Ya ce yanayin rayuwa cikin wadata da almubazzaranci da shugabanni suke yi shi ke tunzura matasan.

KU KARANTA: Yadda 'yan daba suka sace takardun makaranta na, fasfoti da kayan abinci - Dan majalisa

Shugabanni su farka, mulkin kama-karya ne yake fusata matasa - Okorocha
Shugabanni su farka, mulkin kama-karya ne yake fusata matasa - Okorocha. Hoto daga tribuneonlineng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotuna: Harkokin kasuwanci sun koma daidai bayan cire dokar kulle a Jos

Ya ce ya kamata a yanke kaso 50 zuwa 70 na kudaden da ake shaka wa gwamnoni da ministoci, don suma matasa su samu sassauci.

Ya ce yakamata shugabanni su rage yanayin yadda suke kashe kudi yadda suka ga dama, domin wannan zanga-zangar alama ce da matasan ke nuna musu cewa sun gaji.

Ya ce shugabannin kasar nan na nuna son kansu karara wurin tafiyar da mulkinsu, wanda hakan bai dace ba.

A wani labari na daban, a ranar Alhamis ne mai bayar da shawara ga shugaban kasa akan harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno, yace shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce jami'an tsaro su yi aiki daidai iyakar da shari'a ta tsayar da su wurin shawo kan rikicin da ke faruwa a Najeriya.

Monguno ya bayyana hakan ne yayin da manema labaran gidan gwamnati suka yi hira da shi bayan gama taron jami'an tsaro da shugaban kasa ya shirya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel