Kungiyar Oba ta ji haushin amfani da karfin bindiga ga ‘Yan zanga-zanga
- Kungiyar Sarakunan Yarbawa sun soki harbe masu zanga-zanga a Lekki
- Sarakai a Kwara, Kogi, Osun, Oyo, Ondo, Ekiti, Legos, Ogun sun yi jawabi
- Sun ce bai kamata a harbe Bayin Allah da ba su dauke da kayan fada ba
Wannan kungiya ta manyan kasar su na koka wa da abin da su ka kira amfani da karfin bindiga a kan matasan da ba su dauke da makamai.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wannan kungiya ta kunshi Sarakunan gargajiyan da su ka fito daga duka jihohin da ke da Yarbawa a Najeriya.
KU KARANTA: #EndSARS: Ya kamata Shugaban kasa ya yi amfani da hikima – Sultan
Wadannan jihohi kuwa su ne: Osun, Oyo, Ondo, Ekiti, Legos, Ogun, sai kuma Kwara da Kogi.
A wata takarda da sarakan su ka fitar ga ‘yan jarida, sun nuna rashin jin dadinsu game da abin da ake zargin sojoji sun yi a ranar Talata a Lekki, Legas.
Su ka ce: “Ya na da muhimmanci a tuna ba a raba mulkin farar hula da damar mutane na fitowa su yi zanga-zangar lumana domin ba gwamnati shawara.”
“Hakkin yin zanga-zangar lumana ya na cikin damar da aka bada a karkashin kundin tsarin mulkin Najeriya da kundin kare hakkin mutanen Afrika.”
KU KARANTA: INEC ta fasa zabe a Legas da Bayelsa, dsr saboda zanga-zanga
Kungiyar ta kuma ce: “Abin mamaki ne da da-na-sani da takaici a ga wasu sojoji da ba a sansu ba, su na harbin mutanen da su ke kiran gwamnati ta gyara.”
Sarakan a matsayinsu na iyayen kasa, sun bada shawarar a hakura da ramuwa, a zauna ayi sulhu.
Gwamna Dave Umahi hankali ya ce lamarin #EndSARS ya koyawa shugabanni hankali, ya kuma ba matasa hakuri a madadin sauran masu mulki a kasar.
Bayan haka, Umahi ya ba shugabannin shawara su fara jawo matasan Najeriya a jikinsu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng