Harin Lekki: Na kira waya aka ce mani Shugaba Buhari ba ya kusa inji Sanwo-Olu

Harin Lekki: Na kira waya aka ce mani Shugaba Buhari ba ya kusa inji Sanwo-Olu

- An yi hira da Gwamna Babajide Sanwo-Olu game da harin da aka kai a Lekki

- Ya ce ya yi yunkurin ya tuntubi Shugaban kasa amma bai same shi a waya ba

- A karon farko Shugaban kasar ba ya ofis, daga baya kuma aka ce ya shiga taro

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ce ya nemi kiran shugaba Muhammadu Buhari domin ya fada masa ana harbe masu zanga-zanga.

Mista Babajide Sanwo-Olu ya bayyana cewa bai yi nasarar samun shugaban kasar a wayar salula ba, domin kuwa da ya kira, an fada masa ba ya nan.

Babajide Sanwo-Olu ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka yi hira da shi a tashar Arise TV.

KU KARANTA: Kashe ‘yan zanga-zanga zai jawo wa Gwamnati ta gaza sulhu - Obasanjo

Gwamna ya ce: “Na kira shugaban kasa sau biyu a jiya, amma aka fada mani cewa ba ya ofis.”

Sanwo-Olu ya kara da cewa: “Da na kira a karo na biyu, sai aka fadi mani cewa ya na wajen taron mako-mako na majalisar zartarwa (FEC)”

“Ban yi magana da shi ba kai-tsaye, amma na tuntube shi ta ofishin shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa (Farfesa Ibrahim Gambari)” inji sa.

Mai girma gwamnan bai bayyana matakin da gwamnatin tarayya ta dauka ba, amma ya tabbatar da cewa abin da ya auku a ranar ya fi karfin ikonsa.

KU KARANTA: Abin takaici ne a kashe mutane a wajen zanga-zanga - EU

Harin Lekki: Na kira waya aka ce mani Shugaba Buhari ba ya kusa inji Sanwo-Olu
Sanwo-Olu da Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Da ya ke magana game da cire na’urorin daukar hoto a kofar shiga Lekki, ya karyata zargin, ya ce: “Na’urorin daukar hoton da aka cire, ba na tsaro ba ne.”

Sanwo-Olu ya ce na’urorin daukar lambar motoci aka cire, amma sauran na’urorin duk su na nan.

Dazu kun ji cewa babban jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya ce sharri ake yi masa, bai da wani hannu a barkewar zanga-zangar #EndSARS a Najeriya.

Haka zalika tsohon Gwamna Tinubu ya soki harbe ‘yan zanga-zanga da aka yi cikin duhun dare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel