Legas: Rufe manyan kofofin shiga gari ya jawo asarar N234m a cikin kwanaki 10

Legas: Rufe manyan kofofin shiga gari ya jawo asarar N234m a cikin kwanaki 10

- Gwamnatin Jihar Legas ta yi asarar fiye da Naira miliyan 230 a kwana tara

- Zanga-zangar #EndSARS ce ta yi sanadiyyar dakatar da karbar kudin shiga

- A duk rana gwamnatin Legas na tatsar miliyoyin kudi a manyan kofofin gari

A dalilin zanga-zangar #EndSARS da ake yi a jihohin Najeriya, gwamnatin jihar Legas ta tafka asara mai yawan gaske a cikin ‘yan kwanaki.

Gwamnatin jihar Legas ta ce ta rasa akalla Naira miliyan 234 saboda rufe manyan kofofin gari da ta yi a cikin birnin Legas, inji jaridar Punch.

Rahotanni sun ce an yi dace gwamnatin Legas ta cigaba da samun kudin-shiga daga tallace-tallacen da ta ke daukar nauyi a kofofi da kafofin gari.

KU KARANTA: IStandWithBuhari sun bukaci shirya babban tattakin lumana a Abuja

An samu wadannan alkaluma ne daga kamfanin Lekki Concession Company wanda su ke da alhakin daukar nauyin kula da manyan kofofin gari.

Wani kwamishina a gwamnatin Legas da ya nemi a sakaya sunansa, ya yi wa manema labarai bayanin irin asarar da aka yi saboda rufe hanyoyi.

Duk rana gwamnati ta na tatsar Naira miliyan goma a gadar Lekki zuwa Ikoyi. Ana samun fiye da Naira miliyan 16 a kan titin Lekki zuwa Epe a kullum.

Ya ce: “Akalla motoci 80, 000 su ke amfani da manyan kofofin gari a kullum, kudin zai iya yin kasa da haka a cikin mako tun da aka fara zanga-zangar.”

KU KARANTA: Gwamnan Legas ya sa dokar ta-baci, babu fita 24/7

Legas: Rufe manyan kofofin shiga gari ya jawo asarar N234m a cikin kwanaki 10
Gwamna Sanwo Olu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“An rufe kofar Lekki gaba daya, an bude kofar Ikoyi, ana shiga ba tare da an biya kudi ba.”

Tsarin shi ne motoci kirar SUC su kan biya N250, kananan motoci na bada N200 wajen haura gadar Ikoyi, ana biyan N400 zuwa N1000 a titin Lekki-Epe.

A jiya ne ku ka ji cewa masu zaman kaso sun balle daga gidan yarin garin Benin. NCS ta ce ba ta san yawan wadanda su ka kubuce daga kurkukun Beni ba.

Ganin an yi sake a gidan mazan ne gwamnati ta maka dokar ta-baci, aka hana kowa fita a jihar Edo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel