Edo: Ofishin ‘Yan Sanda ya na ci da wuta, ana neman shiga gidan yari a Oko

Edo: Ofishin ‘Yan Sanda ya na ci da wuta, ana neman shiga gidan yari a Oko

- An samu wadanda su ka kona ofishin ‘Yan Sanda a garin Benin dazu nan

- Hakan na zuwa ne bayan Gwamnan jihar Edo ya maka dokar ta-baci yau

- Akwai wasu Tsageru da ake zargin su na gigin sake shiga gidan yarin Oko

Yanzu nan mu ke samun labari daga jaridar The Cable cewa ana zargin miyagu sun kona wani ofishin ‘yan sanda a garin Benin, jihar Edo.

Rahotanni sun ce wasu tsageru sun sa wuta a ofishin rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke Ugbekun, a babban birnin jihar Edo a Najeriya.

A daidai wannan lokaci kuma wasu ‘yan iskan gari sun nufi gidan yari da ke yankin Oko.

KU KARANTA: APC ta ce akwai lauje cikin nadi a tafiyar #EndSARS

Wani wanda abin ya faru a gaban idanunsa, ya shaidawa jaridar cewa dinbin mutane sun taru a gaban gidan yarin da ke hanyar titin jirgin sama.

Ana zargin cewa wadannan miyagun mutane su na yunkurin kutsa kansu ne a cikin gidan yarin, bayan ta’adin da aka yi a jihar a yau da safe.

Wani mutumi ya shaida wa manema labarai cewa ya ji wadanda su ka kutsa gidan yarin na titin Sapele su na maganar kai sabon hari a wani kurkukun.

Ya ce: “Lokacin da ‘yan iskan su ka shiga gidan yarin da ke kan titin Sapele, na ji taron jama’a su na cewa sai mu wuce gidan kurkukun Oko.”

KU KARANNTA: An burma wa ofishin 'Yan Sanda a Legas

Edo: Ofishin ‘Yan Sanda ya kama da wuta, ana neman shiga gidan yari a Oko
Ofishin ‘Yan Sandan Ugbekun Hoto: Port City News
Asali: UGC

Wannan Bawan Allah da abin ya faru a cikin kunnuwansa, ya ce ya yi tunanin wargi matasan su ke yi da ya ji su na wadannan maganganu dazu.

A halin yanzu dokar ta-baci ta na aiki a fadin jihar Edo, babu wanda ake so a gani a cikin gari. Wannan takunkumi zai fara aiki ne daga karfe 4:00.

A yau wasu daga cikin wadannan tsageru su ka shiga gidan mazan da ke hanyar zuwa Sapele, a dalilin haka masu zaman kaso da dama su ka tsere dazu.

Bayan nan kuma an ji cewa jami'an ƴan sandan RRS sun gamu da irin wannan faramaki a Legas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng