Catriona Laing ta shigo Najeriya a karon farko bayan bullar COVID-19

Catriona Laing ta shigo Najeriya a karon farko bayan bullar COVID-19

- Jakadar Birtaniya, Catriona Laing ta zo Najeriya bayan watanni bakwai

- Laing ta hadu da tsohon Gwamna Bola Tinubu, inda su ka tattauna jiya

- Jakadar ta kuma zauna da hukumomin NDLEA da NAPTIP a makon nan

Jakadar Birtaniya, Catriona Laing, ta zo Najeriya a makon nan, har kuma ta samu damar zama da tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Tinubu.

Misis Catriona Laing mai wakiltar gwamnatin Birtaniya a kasar nan ta ce ta hadu da Bola Tinubu ne a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba, 2020.

Laing ta bayyana haka ne a shafinta na Twitter a jiya da safe. Ofishin jakadancin kasar ta ce Jakadar sun tattauna kan wasu batutuwa da Bola Tinubu.

KU KARANTA: Matashin da ya je ci rani a Amurka daga Najeriya ya na neman zama Gwamna

Jakadancin ta ce an yi “Tattaunawa mai fadi game da batutuwan da su ka yi tarayya da Najeriya.

Tun kafin ta iso Legas, Jakadar ta yi amfani da shafinta na @CatrionaLaing1, ta shaidawa Duniya cewa za ta yi zama da babban ‘dan siyasar kasar.

Bola Tinubu ya yi gwamna tsakanin 1999 zuwa 2007 a jihar Legas, kafin nan ya taba zama Sanata, kuma ya na cikin wadanda su ka kafa jam’iyyar APC.

Jakadar ta tabbatar da cewa wannan ne karon farko da ta zo garin Legas a lokacin mai tsowa, tun lokacin da aka barke da annobar COVID-19 a Duniya.

KU KARANTA: An ba Atiku kwanaki 7 ya dawo da tulin Ma’aikatan da ya sallama

Catriona Laing ta shigo Najeriya a karon farko bayan bullar COVID-19
Catriona Laing da Tinubu Hoto; Twitter/UKinNigeria
Asali: Twitter

Misis Laing ta nuna farin cikinta na sake haduwa da mutanen Najeriya a madadin kasar Birtaniya. Laing ta karbi wannan aiki ne a shekarar 2018.

Jakadar ta kuma yi zama da hukumomin NDLEA da NAPTIP domin hana safarar kwayoyi da mutane.

Ku na da labari cewa yanzu haka a Amurka, hukumar nan ta FBI ta samu wasu da ke kokarin hambarar da gwamnonin jihohi daga karagar mulki.

Gwamnar Michigan, Whitmer ta na cikin wadanda miyagu ke nufin tunbukewa daga mulki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng