Atiku Abubakar ya ce Ahmad Bamalli zai iya cike gibin da Shehu Idris ya bari

Atiku Abubakar ya ce Ahmad Bamalli zai iya cike gibin da Shehu Idris ya bari

- Jama’a su na ta magana game da nadin sabon Sarkin Zazzau da aka yi

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi jawabi a jiya

- Kungiyar Gwamnonin Arewa da irinsu Bola Tinubu sun fito da jawabi

Mutane su na ta fitowa su na tofa albarkacin bakinsu game da nadin sarautar da aka yi a birnin Zazzau, bayan rasuwar Alhaji Shehu Idris.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi farin cikin nada Ambasada Ahmad Bamalli a matsayin sabon Sarkin kasar Zazzau.

Alhaji Atiku Abubakar ta bakin Paul Ibe, ya ce Sarki Ahmad Bamalli zai karawa karagar Zazzau daraja ganin irin tafiye-tafiyen da ya yi a Duniya.

Atiku ya ce Sarakin ya na cikin masu karancin shekaru, amma zai iya cike takalman marigayi.

KU KARANTA: Tarihin Ahmad Bamalli wanda ya karya tarihin shekaru 100 a Zazzau

Daga cikin wadanda su ka yi magana har da kungiyar gwamnonin Arewa, inda shugabansu Simon Lalong ya fitar da jawabi na musamman jiya.

Gwamnan Filato ya ce: “Mu na tayaka murnar wannan babbar dama da Ubangiji ya ba ka domin ka yi wa al’umma hidima irin kakanninka.”

Shi ma jagoran jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu ya fitar da jawabi ta bakin babban hadiminsa Tunde Rahman a ranar Laraban.

Bola Tinubu ya jinjinawa Gwamna Nasir El-Rufai, ya ce zabi wanda ya dace a matsayin Sarki.

Atiku Abubakar ya ce Ahmad Bamalli zai iya cike gibin da Shehu Idris ya bari
Sabon Sarkin Zazzau Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: ‘Dan Majalisar Zariya ya karyata rade-radin nada sababbin Masarautu

“Ambasada Bamalli, fitacccen Jakada ne, wanda ya kware a shugabanci, kuma babban mai rike da babbar kujerar sarauta. Ina taya sa murna.” Inji Tinubu.

Tinubu ya ce: “Ina taya Gwamna Nasir El-Rufai murnan nuna hangen nesa wajen yin wannan zabi.”

Sauran wadanda su ka yi magana sun hada shugaban majalisa, Ahmad Lawan, tsohon gwamna, Ahmad Makarfi, Sanatan Kaduna, Abdu Kwari.

A jiya kuma kun ji cewa Alhaji Mohammed Munir Ja'afaru, Yariman Zazzau ya taya sabon sarki Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli murna.

Munir Ja'afaru shi ne Yariman Zazzau, kuma 'yan kan-gaba a takarar sarautar kasar Zazzau.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel