Garambawul: Dattawan arewa sun mara wa Adeboye baya, sun yi korafi cewa Najeriya ta gaza

Garambawul: Dattawan arewa sun mara wa Adeboye baya, sun yi korafi cewa Najeriya ta gaza

- Matsayar Fasto Adejare Adeboye kan garambawul ya samu goyon bayan kungiyar dattawan arewa

- Kakakin kungiyar, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce Najeriya na fuskantar barazanar ballewa idan har ba a magance wasu lamura ba

- A cewarsa, sauya fasalin kasar zai magance korafe-korafe, kawo shawarwari da kuma samar da mafita ga tarin matsaloli daban-daban

Kungiyar dattawan arewa ta goyi bayan matsayar shugaban Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Adejare Adeboye kan sauya fasalin lamura, cewa kasar ta fara gazawa.

Hakeem Baba-Ahmed, kakakin kungiyar, ya bayyana matsayin kungiyar yayinda yake jawabi a wani shirin gidan talabijin na kai tsaye a Lagas a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba.

A cewarsa, lokaci ya yi da ya kamata a sauya fasalin Najeriya domin magance gibin siyasa da kuma korafe-korafen wasu yankuna a kasar.

KU KARANTA KUMA: FG ta bada umurnin sake tantance masu N-Power

Garambawul: Dattawan arewa sun mara wa Adeboye baya, sun yi korafi cewa Najeriya ta gaza
Garambawul: Dattawan arewa sun mara wa Adeboye baya, sun yi korafi cewa Najeriya ta gaza Hoto: @THISDAYLIVE
Asali: Twitter

Legit.ng ta fahimci cewa, matsayar NEF na zuwa ne bayan manyan kungiyoyi a kasar da suka hada da na Afenifere, Ohanaeze da sauransu sun marawa Shugaban cocin RCCG baya kan bukatar magance korafe-korafen kasa ta hanyar yin garambawul.

A tuna cewa Fasto Adeboye, da yake jawabi a wani taro tare da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi da sauran manyan yan Najeriya, ya kaddamar da cewa Najeriya na fuskantar barazanar ballewa idan ba a yi garambawul ba.

Shahararren malamin ya bayyana cewa sauya fasalin lamura ne hanya guda da za a bi domin daidaita abubuwa su dawo daidai.

Baba-Ahmed ya ce:

“Muhimman abubuwa biyu da ya rataya a wuyan kasa sune kare al’umma da kuma samar da jin dadinsu. Yanzu, kasar Najeriya ta gaza a sansanonin biyu. Don haka, a gare mu yin garambawul ne hanyar magance wadannan abubuwa da gano mafita, shawarwari da sauye-sauye da zai dace da tsarin inganta su.

KU KARANTA KUMA: Ganduje ya rantsar da sabbin kwamishinonin KANSEIC uku da sakatarorin dindindin hudu

“Akwai bukatar mu yi duba ga kundin tsarin mulkinmu, duba hanyar samar da abubuwan da suka kamata ga kasar Najeriya, mika hakkoki a mulki, ayyukan manyan hukumomi, ko kuma gazawar manyan hukumomi wajen aiki da kuma yadda za mu iya inganta su.”

A wani labarin, Alhaji Tanko Yakasai ya ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba shi da ikon sauya fasalin tsarin mulkin Najeriya a karkashin kundin tsarin mulkin kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel