Dan majalisar wakilai ya fasa kwai, ya bayyana kudin albashin da ake biyansu

Dan majalisar wakilai ya fasa kwai, ya bayyana kudin albashin da ake biyansu

- Bayan shekara da shekaru, an samu dan majalisan da ya bayyana kudin albashin da ake biyan yan majalisa

- Honarabul Karu bai fadi hakan ba tare da kalubale daga wani abokin aikinsa ba a taron

- Yan majalisan na tsoron kada mutane su san adadin kudin da suke samu a ofis

Dan majalisa mai wakiltan mazabar Kaltungo/Shongom a majalisar wakilan tarayya, Simon Karu, ya bayyana adadin kudin da shi a abokan aikinsa ke samu kowani wata.

Karu yace bayan kudin albashi N800,000, da kowanne cikinsu ke samu, ana basu milyan 8.5 kudin harkokin yau da gobe a kowani wata.

Yawancin masu sukan tsarin amfani fa majalisun dokoki biyu na haka ne saboda irin bannar kudin da akeyi wajen biyansu albashi da alawus.

Suna ganin cewa majalisa daya kadai Najeriya ke bukata domin rage kudin da ka kashewa. Amma wasu na ganin cewa kawai a rage musu albashi.

Amma a fasa kwan da dan majalisa, Simon Karu, yayi ranar Alhamis a cibiyar taro na tunawa da Umar Musa Yar'adua dake Abuja, ya bayyana irin makudan kudin da suke karba.

DUBA NAN: Kundin Tarihi: Jerin abubuwa masu muhimmanci 20 da suka faru daga 1960 zuwa 2020

Dan majalisar wakilai ya fasa kwai, ya bayyana kudin albashin da ake biyansu
Credit: @HouseNGR
Source: Twitter

KU DUBA: Hankali ba zai dauka ba ace Saudi ta fi Najeriya arahar man fetur - Buhari

Yace, "Albashin mamban majalisar wakilai da har da ni muke karba a wata N800,000 ne."

"Na fada muku zan fasa kwan..., kudin harkokin yau da goben dan majalisar wakilai milyan 8.5 ne. Wadanda suka sani sun san abinda nike fada haka ne."

"Matsalan shine bukatun da al'ummarmu ke gabatarwa gabanmu kuma idan ka gaza haka kuma, zasu fara gaya maka magana."

"Kafin in shigo nan, na samu sakonni uku daga al'umman mazabata suna neman kudi da aiki. Idan baka yi ba, sai a samu matsala,"

Amma shugaban kwamitin yarjejeniya na majalisar wakilai, Ossai Nicholas Ossai, ya bayyanawa mutanen dake taron cewa ba gaskiya abokin aikinshi, Hanarabul Karu, ke fada ba.

"Ban taba samun irin wannan albashin ba tun na zo majalisar dokokin tarayya, kuma na riga shi zuwa majalisa," Yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel