Najeriya ta rubuta takarda zuwa ga Xi Jinping domin taya Sinawa murna

Najeriya ta rubuta takarda zuwa ga Xi Jinping domin taya Sinawa murna

- Muhammadu Buhari ya rubutawa mutanen kasar Sin wasika a Ranar Lahadi

- Shugaban Najeriya ya taya mutanen Sin murnar zagayowar ranar farin cikin

- Buhari ya aika wannan wasika ne a madadin mutane da gwamnatin Najeriya

A ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2020, shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta takarda zuwa ga Xi Jinping na kasar Sin domin taya sa murna.

Shugaban Najeriyar ya aika takarda ta musamman ne domin taya Sinawa murna a ranar da su ke bikin cika shekara 71 a Duniya da zama kasa mai iko.

Mutanen kasar Sin su kan yi biki na musamman a ranar 1 ga watan Oktoba na kowace shekara.

KU KARANTA: Jonathan da Shugaban kasa Buhari sun sa labule a Aso Villa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a wasikar da ya rubuta, ya ce dankon abokantakar Najeriya da kasar ta Sin ta na cigaba da kara karfi a shekarun nan.

Buhari ya ke cewa ko da ya ke annobar COVID-19 ta jawowa tattalin arzikin Duniya cikas, kasar Sin ta jajirce sosai, kuma ta taimakawa sauran kasashe.

A wasikar da ya rubuta, shugaban na Najeriya ya godewa gwamnatin kasar Sin na yadda ta ke taimakawa kasarsa wajen gina abubuwan more rayuwa.

KU KARANTA: Buhari ya sanar da wasu nadin mukamai

Najeriya rubuta takarda zuwa ga Xi Jinping domin taya Sinawa murna
Wasikar Buhari ga Sinawa Hoto: Daily Post
Source: UGC

“A lokacin da ku ke bikin cika shekara 71, ina mai aika maku sakon gaisuwa a madadin kai na, gwamnati da mutanen tarayyar Najeriya.” Inji shugaba Buhari.

“Ina taya Sinawa a gida da waje murnar wannan lokacin farin ciki. Tun daga lokacin da alaka ta fara shiga tsakanimu shekaru 40 da su ka wuce, kara karfi ta ke yi.”

Wannan takarda da wasunta sun fito ne a makon nan ta hannun Mista Femi Adesina, mai taimakawa shugaban kasar wajen yada labarai da hulda da jama’a.

Buhari ya kuma taya Farfesa Tijjani Bande murnar kammala aiki da majalisar dinkin Duniya.

A gida Najeriya kuma, mun ji cewa Gwamnatin Tarayya za ta raba motocin haya, domin a rage radadin karin kudin fetur da aka yi.

George Akume ya ce wannan zai taimaka wajen ceto mutane miliyan 100 daga talauci a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel