‘Yan bindiga sun shiga Jihar Katsina, sun sace mutane 4, an ji wa 1 rauni
- ‘Yan bindiga sun aukawa Jihar Katsina, sun sace mutum 4 a makon nan
- An yi garkuwa da Yayar, Ahmed Musa Dangiwa a gidanta da ke Kankia
A wasu mabambantan hare-hare, mun ji cewa ‘yan bindiga sun kutsa jihar Katsina, inda su ka yi garkuwa da mutane a cikin tsakiyar makon nan.
Daily Trust ta ce daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, har da ‘yaruwar shugaban bankin bada bashin ginin gida, Arch. Ahmed Musa Dangiwa.
Ahmed Musa Dangiwa ya na cikin manyan jagororin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Katsina.
Wadannan miyagu sun shiga har gida ne sun sace Asiya Dangiwa a farkon ranar Laraba, 23 ga watan Satumba, 2020, a garin Kankiya, a jihar Katsina.
KU KARANTA: Bam ya kashe wasu yara a Malumfashi
Kakakin ‘yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da cewa an sace Hajiya Asiya Dangiwa, ya kuma tabbatar da cewa su na kokarin ganin sun ceto ta.
Jami’in ‘dan sandan ya fadawa ‘yan jarida cewa: “Zan iya tabbatar da aukuwar wannan lamari a garin Kankia, amma mu na yunkuri ganin mun ceto ta.”
Jaridar ta ce an kuma sace wani ma’aikacin kiwon lafiya na gwamnati, Aminu Shaaibu. Shi ma an dauke shi ne a gidan shi a Mairuwa da ke yankin Faskari.
Rahotanni sun tabbatar da ‘yan bindigan sun shiga karamar hukumar Faskari ne a ranar Litinin.
KU KARANTA: Wasu wadanda aka jikkata sun koma gida a Katsina
Abin bai tsaya nan ba, a karamar hukumar Dandume, an ji wa wani Bawan Allah rauni, sannan kuma miyagun sun tsere da kananan yara biyu a makon nan.
Kawo yanzu babu wani labari game da wadanda aka yi garkuwa da su. Jami’an tsaro sun ce ba su da cikakken bayani a kan hare-haren da aka kai a garuruwan.
“Ku ba ni lokaci in tabbatar da faruwar lamarin.” Inji mai magana da bakin ‘yan sandan jihar a lokacin da manema labarai su ka nemi jin ta bakinsa a jiya.
Kwanakin baya kun ji cewa shugaban rundunar sojojin kasa, Janar Tukur Buratai, ya kaddamar da wani atisaye mai taken Ofireshon Sahel Sanity, a jihar Katsina.
Amma a lokacin da ake kaddamar da wannan shiri, sai da 'yan bindiga su ka kai hari a yankin.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng