Idan aka bani dama: Ina da burin zama shugaban kasar Nigeria a 2023 - Okorocha

Idan aka bani dama: Ina da burin zama shugaban kasar Nigeria a 2023 - Okorocha

- Rochas Okorocha ya magantu kan kudirinsa na son zama shugaban kasa a 2023

- Tsohon gwamnan na jihar Imo ya ce yana da burin yiwa yan Najeriya hidima ta wannan bangaren

- Okorocha ya nusar da al’umma cewa takarar kujerar bai da nasaba da kabilanci ko addini, illa cancanta

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya nuna aniyarsa na son takarar kujerar shugaban kasa a zaben shugaban kasa na 2023.

Okorocha ya bayyana cewa dalilinsa na son neman kujerar ya kasance saboda bukatar magance matsalolin rashin tsaro, talauci da dawo da hadin kan kasa, jaridar The Guardian ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: APC ta yi rashi: Kotun zaɓe ta soke nasarar dan majalisar tarayya, ta buƙaci sabon zabe

Ya jaddada cewa:

“Takarar da zan yi na shugabancin kasa ba wai don kawai ina son zama shugaban kasa bane. Idan zan zama shugaban kasa da zai gaza ko shugaban kasa da ba zai cimma nasara ba, toh bana son zama shugaban kasa. Amma idan shugabancina zai kawo hadin kan wannan kasa, toh ina son zama shugaban kasa.

“Idan shugabancina zai magance lamarin talauci da rashin tsaro, toh ina son zama shugaban kasa. Idan shugabancina zai daidaita tattalin arzikin kasar nan da zai sa mu dunga magana kamar sauran kasashe da suka ci gaba, toh ina son zama shugaban kasa. Sannan idan shugabancina zai samar da ilimi ga talakawa, toh zan so zama shugaban kasa. Baya ga wadannan, ku rike shugabancinku da fadar shugaban kasa, bana so.”

Idan aka bani dama: Ina da burin zama shugaban kasar Nigeria a 2023 - Okorocha
Idan aka bani dama: Ina da burin zama shugaban kasar Nigeria a 2023 - Okorocha Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Tsohon gwamnan ya fayyace cewa zama shugaban kasa bai da nasaba da addini ko kabilanci.

KU KARANTA KUMA: Wadatar da kasa da abinci: Buhari ya zabtare farashin taki a Nigeria

“Na kasa ganewa ko mutane na takarar kujerar shugabancin Najeriya ne saboda daga yankin da suka fito ko kuma saboda abubuwan da za su iya yiwa kasar – Ina ganin akwai banbanci tsakanin wadannan abubuwan guda biyu.

“Wasu lokutan, idan muka yi magana game da shugabanci sai mu dauke shi kamar yankin da ka fito da addini ne zai baka canantar neman kujerar ba wai aikin da za ka iya yiwa mutane ba, a nan ne na banbanta."

A wani labarin, Rochas Okorocha, ya yi magana kan rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar APC mai mulki, biyo bayan kaye da ta sha a zaben gwamnan Edo.

Okorocha, sanata mai wakiltan yankin Imo ta yamma, ya ce APC ta kare, cewa abunda ya rage ma jam’iyyar shine mutuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ake gani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng