Watakila Gwamnatin Zamfara ta shiga Kotu da Yari saboda zargin cin kudin hanyoyi
- Gwamnatin Zamfara ta ce Abdulazizi Yari ya yi awon gaba da Naira Biliyan 37
- Kwamishina ya ce gwamnatin tarayya ta biya Zamfara kudin titunan da ta yi
- Wannan kudi ba su cikin asusun jihar Zamfara a halin yanzu inji Kwamishinan
Ana zargin tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari, da laifin karkatar da wasu kudi daga asusun gwamnati a lokacin ya na kan mulki.
Naira biliyan 37.8 ake zargin Abdulaziz Yari ya yi awon-gaba da su daga kudin wasu ayyuka da gwamnatin tarayya ta dawowa jihar Zamfara da su.
Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar 23 ga watan Satumba, 2020, cewa wannan bayani ya fito ne daga bakin kwamishinan kudi, Rabi’u Garba.
Alhaji Rabiu Garba ya ce gwamnatin Mai girma Abdulaziz Yari ta yi aikin hanyoyin gwamnatin tarayya na Naira biliyan 47 tun daga 2011 zuwa 2018.
KU KARANTA: An kama na kusa da Yari da zargin alaka da 'Yan bindiga
A cewar kwamishinan kudin mai-ci, gwamnatin tarayya ta maidawa gwamnatin Zamfara wasu kudin da ta kashe wajen yin aikin titunan tarayya.
Garba ya ce, “Yari a takardun barinsa a ofis, ya bayyana cewa wadannan kudi Naira biliyan 47.8bn na gyara da fada titunan gwamnatin tarayya ba su shigo asusun gwamnati ba har ya bar ofis.”
“Amma da mu ka rubutawa ma’aikatar ayyuka ta tarayya takarda domin a dawo mana da wannan kudi, sai mu ka gano cewa an biya Yari Naira biliyan 37.”
Kwamishinan, a madadin gwamnatin Bello Matawalle ya roki gwamnatin tarayya da kasashen ketare da jami’an tsaro, su sa a karbowa jihar wadannan kudi.
KU KARANTA: Shugaban APC ya watsawa ‘Dan takararsu kasa a ido a zaben Edo
Rabiu Garba ya nemi a karbo wadannan makudan biliyoyi daga hannun tsohon gwamnan ne domin a samu damar yi wa al’ummar Zamfara ayyukan more rayuwa.
Jaridar ta ce ta yi kokarin jin ta bakin Yari, amma abin ya fasakara. Wani jigon APC a Zamfara, Alhaji Sani Gwamna, ya karyata zargin, ya ce ba gaskiya ba ne.
Kwanaki kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Zamfara ta kafa wani kwamiti na musamman da zai binciki kwangilar gina sabon gidan gwamnati a lokacin APC.
Majalisar ta nada mutane bakwai da su binciki kwangilar da Abdulaziz Yari ya bada.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng