Yadda dan majalisa ya shiga daji da kansa ya ceto yan mazabarsa da yan bindiga suka sace a Kwara

Yadda dan majalisa ya shiga daji da kansa ya ceto yan mazabarsa da yan bindiga suka sace a Kwara

- Dan majalisar dokokin jihar Kwara Gwanabe-Danmi- Adera ta yankin karamar hukumar Kaiama Hon Sa’idu Baba Ahmad ya jagoranci tawagar tsaro zuwa daji

- A yayin sintirin, sun yi nasarar ceto mutanen mazabarsa guda 13 da yan bindiga suka yi garkuwa dasu

- Sun kuma kashe yan bindiga hudu a yayin musayar wuta da suka yi

Hon Sa’idu Baba Ahmad, dan majalisar Kwara mai wakiltan mazabar Gwanabe-Danmi- Adera ta yankin karamar hukumar Kaiama kuma mamba a kungiyan sintiri na Miyetti Allah, ya jagoranci wata tawagar yan sintiri da jami’an tsaro zuwa daji.

A cikin haka, sun yi nasararkubutar da wasu mutane 13 yan mazabarsa wadanda yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Har ila yau tawagar sun kuma yi nasarar halaka yan bindiga hudu a yayin musayar wuta da suka yi dasu.

Dan majalisar ya bayyana cewa sun kwashe tsawon kwanaki suna aikin sintiri a cikin jejin Old Oyo National Park kafin su tarar da yan bindigar, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Yadda dan majalisa ya shiga daji da kansa ya ceto yan mazabarsa da yan bindiga suka sace a Kwara
Yadda dan majalisa ya shiga daji da kansa ya ceto yan mazabarsa da yan bindiga suka sace a Kwara Hoto: Gettyimages/Kwara State House
Source: Getty Images

A cewarsa, sun shafe kwanaki uku suna shiga jeji suna farautar yan ta’addan inda daga baya suka yi nasarar ceto mutane 13 da suka yi garkuwa da su.

KU KARANTA KUMA: Har yanzu yana cikinmu: APC ta ƙaryata jita jitar fatattakar Oshiomole daga jam'iyyar kwata kwata

Sa'idu ya kara da cewa babu mutum ko guda da ya ji rauni a cikin wadanda suka kubutar, cewa dukkansu suna cikin koshin lafiya, sannan sun kai wadanda suka nuna alamar galabaita asibiti ana duba su.

Ya ce: ''Mun samu gawawwaki hudu a cikin 'yan bindigar, kana mun kwato bindigogi ƙirar AK 47 da kwanson harsasai shida da harsasai guda 67."

Sai dai ya ce basu yi nasarar kama sauran 'yan bindigar ba wanda adadinsu su tara ne, amma kuma cewa biyu daga cikinsu sun tsere da raunukan harsasai.

Ya ce sun samu wannan nasara ne ta hanyar gangamin hadin gwiwa da 'yan sintiri na Fulani da Yarbawa, sojoji da yan sanda har da shugaban karamar hukumar Kayama.

''Sai da muka kasu gida biyu da tawagarmu da ta jami'an tsaro, amma tawagarmu ce ta yi arangama da su.

''Muhimmancin wannan sintirin da muka yi shi ne muddin muka bari suka yi kaka gida a wajen za su hana mutanenmu walwala, amma Alhamdlillahi da muka tarwatsa su yanzu za a samu zaman lafiya,'' cewar shi.

Dan majlisar ya bayyana cewa dama tun dama chan shi dan kungiyar Miyetti Allah ta jihar Kwara ne tun kafin ya san zai zama dan majalisa.

Ya kuma rike muƙamin sakataren kungiyar har na tsawon shekara takwas yana kuma gudanar da ayyukan sintiri a cikin kungiyar.

KU KARANTA KUMA: Zulum ya bawa iyalin marigayi Kanal Bako kyautar gida da N20m (Hotuna)

Daga karshe ya ce sun mika gawawwakin 'yan bindigar hudu da suka rasa rayukansu a rangaramar ga rundunar ƴan sandan Najeriya.

A wani labarin kuma, 'Yan bindiga sun kashe hakimin Feron a karamar hukumar Barkin Ladi na jihar Plateau, Bulus Chuwang Jang a harin da suka kai da yammacin ranar Litinin.

Shugaban matasan Berom a Heipang da ke makwabtaka da Barkin Ladi, Rwang Tengwong ya tabbatar wa The Punch afkuwar lamarin a Jos a ranar Talata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel