Zaben Edo: Mu na taya Obaseki, mutanen Edo da ‘Yan kasa murna inji APC

Zaben Edo: Mu na taya Obaseki, mutanen Edo da ‘Yan kasa murna inji APC

- APC ta taya Gwamna Godwin Obaseki murnar lashe zaben Jihar Edo

- Shugaban rikon kwarya na Jam’iyyar ya ce babu wani magudi a zaben

- Wannan magana ta ci karo da ikirarin da ‘Dan takarar APC ya ke yi

Jam’iyyar APC ta fitar da jawabi bayan an sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Edo wanda aka gudanar a ranar 19 ga watan Satumba, 2020.

APC ta taya Gwamna Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP murnar lashe wannan gagarumin zabe.

Wannan jawabi ya fito ne daga bakin shugaban rikon kwarya na jam’iyyar mai mulki, Alhaji Mai Mala Buni a ranar Litinin, 21 ga watan Satumba.

Gidan talabijin na Channels ta ce Mai Mala Buni ya fitar da wannan jawabi da taken “Zaben gwamnan jihar Edo: Nasara ga damukaradiyya.”

KU KARANTA: APC ta na zargin Fayemi ya marawa Obaseki baya a zaben Jihar Edo

A jawabin shugaban APC na wuce-gadin, hukumar shirya zabe na kasa watau INEC ta yi zaben gaskiya, ya nuna murdiya da magudin zabe ba su yi aiki ba.

Buni ya ce, “An kammala zaben gwamnan jihar Edo, hukumar INEC ta sanar da wanda ya yi nasara a matsayin Mista Godwin Obaseki. ‘dan takarar jam’iyyar PDP.”

Jawabin ya kara da cewa: “Don haka mu na taya wanda ya lashe wannan zabe murna, da mutanen jihar Edo da kuma daukacin ‘yan Najeriya.”

“Yadda aka yi zaben kuma aka sanar da sakamako cikin kwanciyar hankali ya na nufin damukaradiyya ce ta yi nasara.”

Zaben Edo: Mu na taya Obaseki, mutanen Edo da ‘Yan kasa murna inji APC
'Dan takarar APC ya na ganin an yi magudi a Edo
Source: UGC

KU KARANTA: Edo: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da Ganduje da Mai Mala Buni

Buni ya ce APC za ta cigaba da marawa gwamnatinsu da shugaba Buhari ya ke jagoranta baya.

A matsayinmu na jam’iyya, mu na taya shugabanmu, Muhammadu Buhari GCFR wajen tabbatar da shirinsa na ganin an yi zabe na gari mai inganci domin habaka tubulin siyasarmu.

Idan za ku tuna Gwamna Obaseki ya samu kuri’a 307,955, inda ya tika Fasto Osagie Ize-Iyamu na jam’iyyar APC mai kuri’a 223,619 da kasa.

Irinsu Godwin Erhahon, su na ganin cewa Adams Oshiomhole ya sa jam’iyyar APC ta sha kashi a Edo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel