Cirko cirko: Kowa ya nutsu, yana jiran sakamakon zaben jihar Edo

Cirko cirko: Kowa ya nutsu, yana jiran sakamakon zaben jihar Edo

- Al'ummar jihar Edo da ma daukacin Nigeria na ci gaba da zaman jiran sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar

- A jihar Edo, akwai kananan hukumomi 18, gundumomi 192 da kuma rumfunan zabe 2,627

- Ya zuwa yanzu, hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumo 16, inda PDP ta lashe 11, yayin da APC ta lashe 5

Zaman cirko cirko na ci gaba da kamari daga jiya zuwa yau, a yayin da hukumar INEC ke ci gaba da sanar da sakamakon zaben zaben gwamnan Edo da aka gudanar a ranar Asabar.

A jihar Edo, akwai kananan hukumomi 18, gundumomi 192 da kuma rumfunan zabe 2,627.

Kamar yadda sakamakon zaben ke nunawa, takun sakar na gudana ne tsakanin gwamna Godwin Obaseki na jam'iyyar PDP da kuma Pastor Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar APC.

KARANTA WANNAN: Zaben Edo: Jami'in tattara zabe na karamar hukumar Orhionmwon ya yi batan dabo

Cirko cirko: Kowa ya nutsu, yana jiran sakamakon zaben jihar Edo
Cirko cirko: Kowa ya nutsu, yana jiran sakamakon zaben jihar Edo
Source: Twitter

Zaben, wanda al'ummar jihar suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka kada kuri'unsu, ya fuskanci tarnaki daga yan bangar siyasa a wasu rumfunan zabe.

Daga cikin kananan hukumomin da aka tayar da rikici a zaben, akwai Orhiomwon, Owan ta Yamma, Egor, Ikpoba-Okha, Ovia ta Kudu maso Yamma da kuma Oredo.

Haka zalika, an samu tangarda da na'urorin tantance masu kada kuria, kamar yadda Obaseki da Adams Oshiomhole su ka yi korafi, sai kuma rashin isowar sakamakon zabe da wuri.

KARANTA WANNAN: Muhimman abubuwa 5 da suka faru a ranar da aka gudanar da zaben Edo

Daga sakamakon kanana hukumomin da hukumar INEC ta karanto, na nuni da cewa Obaseki, Ize-Iyamu, Oshiomhole da Philip Shaibu, sun kawo akwatinansu.

Haka zalika, sakamakon zaben ya nuna cewa Gwamna Obaseki ke kan gaba, da tazarar kuri'u masu yawa.

Ga sakamakon zaben kananan hukumomin:

Karamar hukumar Igueben APC: 5,189 PDP: 7,870

0:55 AM Karamar hukumar Esan ta Arewa maso gabas APC 6559 PDP 13,579

0:59 AM karamar hukumar Esan ta tsakiya PDP: 10,694 APC: 6,719

6:42 AM karamar hukumar Ikpoba Okha PDP: 41, 030 APC: 18, 218 Tazara: 22,812

6:43 AM karamar hukuma Owan ta gabas APC: 19,295 PDP: 14,762

6:45 AM karamar hukumar Estaka West APC: 26,140 PDP: 17,959

6:46 AM karamar hukumar Egor APC: 10, 202 PDP: 27, 621

6:48 AM karamar hukumar Esan ta yamma APC - 7,189 PDP - 17,433

6:51 AM karamar hukumar Uhunmwonde PDP: 10,022 APC: 5,972

7:31 AM Karamar hukumar Ovia ta Arewa APC - 9907 APGA - 15 PDP - 16, 987 SDP - 36 ZLP - 12

7:43 AM Karamar hukumar Esan south East APC: 9,237 PDP: 10,563

7:50 AM karamar hukumarsa Oredo APC: 18,365 PDP: 43,498

8:09 AM Karamar hukumar Owan West APC - 11,193 PDP - 11,485

10:44 AM APC ta lashe zaben Karamar hukumar Etsako Central APC - 8359 PDP - 7478

11:25 AM Karamar hukumar Akoko Edo APC -- 22,963 PDP -- 20,101

11:25 AM Karamar hukumar ETSAKO-EAST APC: 17,011 PDP: 10,668

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel