Da duminsa: Najeriya ta tabbata cibiyar mutuwar yara masu kasa da shekaru 5 a duniya

Da duminsa: Najeriya ta tabbata cibiyar mutuwar yara masu kasa da shekaru 5 a duniya

Najeriya ta sha gaban kasar India a matsayin babbar cibiyar mutuwar kananan yara masu kasa da shekaru biyar, kamar yadda majalisar kula da kananan yara ta duniya ta bayyana a 2020.

Wannan cigaban ya faru kasa da shekaru biyu da bankin duniya ta yi hasashen aukuwarsa.

A 2018, bankin duniya ta ce Najerya zata sha gaban kasar India a yawan mace-macen kananan yara masu kasa da shekaru biyar amma sai 2021.

Kamar yadda bankin duniyan ya bayyana, kasar India ta samu kiyasin mutuwar a kalla kananan yara 989,000 a 2017, yayin da Najeriya ke da 714,000 a wannan shekarar.

Kamar yadda rahoton UNICEF ya bayyana, ya ce Najeriya ta samu mutuwar yara masu kasa da shekaru biyar 858,000 a 2019, yayin da India ta samu 824,000 a 2019, inda ta kasance a mataki na biyu a duniya.

Rahoton wanda ya duba shekaru goma-goma, ya bayyana cewa kashi 49 na mutuwar kananan yara masu kasa da shekaru 5 a duniya yana faruwa ne a kasashe biyar a duniya. Sune: Najeriya, India, Pakistan, Kongo da Ethiopia.

"Najeriya da India kadai suna da kashi daya bisa uku na dukkan mace-macen kananan yara a duniya," rahoton yace.

Da duminsa: Najeriya ta tabbata cibiyar mutuwar yara masu kasa da shekaru 5 a duniya
Da duminsa: Najeriya ta tabbata cibiyar mutuwar yara masu kasa da shekaru 5 a duniya. Hoto daga reviewsgeek
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Za'a yiwa daliban jihar Ogun karin aji kai tsaye ba tare da sun zana jarrabawa ba idan suka koma makaranta a ranar 21 ga watan Satumba - Dapo Abiodun

Rahoton ya kara da cewa, mace-macen yara masu shekaru kasa da biyar ya ragu da a kalla kashi 60 tun daga 1990.

Amma kuma, majalisar dinkin duniya ta bayyana damuwarta a kan yuwuwar dawowar mace-macen kananan yaran a 2020. Hakan babban kalubale ne ga nasarar da aka samu a baya.

"A yayin da har yanzu ba a san illar da kuma yawan mutuwar kananan yara da matasa da cutar korona ta janyo ba, yuwuwar cigaba da mace-macen kananan yara a 2020 abun tsoro ne," yace.

“Yawan mutuwar kananan yaran ta ragu da kusan kashi 60 tun daga 1990 zuwa 2019. Amma kuma akwai babban kalubale a wannan shekarar.

“Duk da wannan cigaban, yara miliyan 5.2 na rasuwa kafin su cika shekaru biyar a 2019 kadai. Abun takaicin shine yadda yaran ke mutuwa sakamakon cutukan da za a iya magancewa."

A wani labari na daban, hukumar kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce wani yaro dan shekara bakwai, Umar Ado ya mutu a cikin rijiya a Unguwa Uku by Yarabawa Street a karamar hukumar Tarauni na jihar.

Sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun hukumar, Alhaji Saidu Mohammed a ranar Laraban wannan makon kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mohammed ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da yamma a lokacin da marigayin ya tafi rijiyar domin ya diba ruwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel