Mai Martaba Bayero ya samu karin matsayi yayin da ya ke halartar taron Kaduna

Mai Martaba Bayero ya samu karin matsayi yayin da ya ke halartar taron Kaduna

Sarkin Kano Mai martaba, Aminu Ado Bayero ya halarci taron majalisar sarakunan gargajiya na yankin Arewacin Najeriya da aka shirya a garin Kaduna

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa Alhaji Aminu Ado Bayero da wasu daga cikin takwarorinsa na kasar Arewa sun samu zuwa wajen wannan babban taro.

An yi wannan zama ne a Ranar Litinin, 7 ga watan Satumba, 2020 a babban dakin taro na Lugard Hall da ke garin Kaduna, inda aka tabo batun rashin tsaro.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya yi jawabi a taron, Sultan ya yi tir da yadda mutane su ke kashe kansu a kudancin Kaduna.

KU KARANTA: Wasu Dattawan Arewa sun roki Shugaban kasa ya tsige Hafsun Soji

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya halarci taron, kuma ya yi magana game da rikicin kudancin jihar da ya ce an shafe shekaru 40 ana fama shi.

Mai martaba sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya na cikin wadanda su ka halarci taro, ya kyankyasa ado cikin farar babbar riga da rawani mai kunne biyu da ya saba.

Mai Martaba Bayero ya samu karin matsayi yayin da ya ke halatar taron Kaduna
Sarki Aminu Bayero a Kaduna Hoto: HRH Bayero
Source: Twitter

An ga Aminu Ado Bayero tare da wasu Sarakai su na raha a wajen wannan taro. Kamar yadda mu ka samu labari ya zauna ne kusa da Mai martaba Shehu Idris.

Rahotanni daga shafin Mai martaban sun bayyana cewa ya kai wa Shehun Borno, Shehu Abubakar Umar Ibn Garbai ziyara ranar da ya isa Garin Kaduna.

KU KARANTA: Sanusi II ya kai ziyara Kaduna bayan ya fito daga Legas

Zuwan Aminu Ado Bayero ya zo ne kusan makonni biyu da tafiyar tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, wanda ya shafe kwanaki biyar a garin Kaduna.

A lokacin da ake wannan taro, sai aka ji an yi wa dokar masarautar Kano garambawul ta yadda Mai girma Sarkin Kano ya zama shugaban majalisar Sarakuna na din-din-din.

A wannan bidiyo kuma za a ga fitowar Sarkin a jiya tare da fadawansa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel