Buhari ya mikawa gwamnan Ondo tutar takara karo na biyu karkashin jam'iyyar APC

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin manyan jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress APC ranar Juma'a, 2 ga watan Satumba, a fadar shugaban kasa ta Aso Villa.

Jigogin jam'iyyar sun kawo masa ziyara ne domin gabatar da masa dan takaran kujeran gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar kuma gwamnan jihar dake kai yanzu, Oluwarotimi Akeredolu.

Daga cikin wadanda suka kai shi akwai shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni; da shugaban kwamitin kamfen zaben jihar Ondo kuma gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-olu.

Hakazalika akwai shugaban gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu; da gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong.

Bayan tattaunawarsu, shugaba Buhari ya mika tutar amincewa da takarar ga gwamna Akeredolu.

Gwamna Rotimi Akeredolu ya lashe zaben fidda gwamnan jam'iyyar APC inda ya doke sauran abokan hamayyarsa.

Wa'adin Akeredolu na farko zai kare ranar 23 ga Febrairu, 2020.

Hukumar gudanar da zabe INEC ta ce an shirya zaben gwamnan jihar Ondo ne ranar 10 ga Oktoba, 2020.

Kalli hotunan:

Buhari ya mikawa gwamnan Ondo tutar takara karo na biyu karkashin jam'iyyar APC
Buhari ya mikawa gwamnan Ondo tutar takara karo na biyu karkashin jam'iyyar APC
Source: UGC

Source: Twitter

Source: Legit

Tags:
Online view pixel