Saboda rashin gaskiya ne ƴan Arewa ke mulkar ƴan Kudu - Shehu Sani

Saboda rashin gaskiya ne ƴan Arewa ke mulkar ƴan Kudu - Shehu Sani

- Arewacin Najeriya na samun damar mulkar kasar ne saboda rashin yarda da ke tsakanin kudu maso gabas da kudu maso yamma

- Wannan ne dalilin da yasa yankin arewa za ta ci gaba da samar da shugaban kasa a a kasar

- Wannan ra’ayi ne na Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya

Shehu Sani, tsohon sanatan Najeriya mai wakiltan Kaduna ta tsakiya ya bayyana ra’ayinsa kan dalilin da sa yake ganin arewa za ta ci gaba da samar da shugaban kasa.

Da yake magana a wani shirin safe a AIT, Sani ya bayyana cewa arewa na amfana a siyasance daga rashin jituwa da rashin aminci da ke tsakanin kudu maso yamma da kudu maso gabas.

Sani ya ce zancen gaskiya a yanzu shine cewa yankunan kudancin kasar biyu sun gwammaci su hade da arewa wajen neman shugabanci fiye da ace sun hada kai da junansu wajen fitar da dan takarar shugaban kasa guda gabannin zaben 2023.

Saboda rashin gaskiya ne ƴan Arewa ke mulkar ƴan Kudu - Shehu Sani
Saboda rashin gaskiya ne ƴan Arewa ke mulkar ƴan Kudu - Shehu Sani
Source: UGC

Ya bayyana cewa rashin yarda da rashin hadin kai da ke kudu ya kasance ne sakamakon yakin basasa na 1967-1970 da kuma manufofin shugabannin da suka gabata.

Sani ya fayyace cewa idan har hakan ya ci gaba da kasancewa a kasar, yankin arewa za ta ci gaba da cin moriyar lamarin gaba daya.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, ya bayyana cewa babu bukatar a fara magana game da wanda za’a mika wa shugabancin kasa a 2023 tunda har yanzu Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a kan kujerar.

Uzodinma ya yi magana a ranar Talata, a fadar Shugaban kasa da ke Abuja, bayan wani taro don neman taimakon shugaba Buhari kan lamuran jiharsa.

Musamman matsalar yashewar kasa da kuma yi wa shugaban kasar godiya a kan ayyukan da ke gudana a yankin kudu maso gabas.

Gwamnan ya ce tunda Najeriya na amfani da damokradiyyar jam’iyyu ne ba wai damokradiyyar kabilanci ba, aikin jam’iyyun ne su yanke hukunci.

Ya ce sune za su yanke shawarar abubuwan da za su duba wajen zabar ‘yan takararsu na shugaban kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel