Atiku ya yi martani yayinda hatsarin mota ya kashe magoya bayan PDP 15 a Zamfara

Atiku ya yi martani yayinda hatsarin mota ya kashe magoya bayan PDP 15 a Zamfara

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya aika sakon ta’aziyya ga gwamnatin jihar Zamfara kan mutuwar magoya bayan PDP a jihar

- Magoya bayan PDP sun mutu a wani hatsarin mota da ya wakana bayan sun yi wa Gwamna Matawalle maraba da zuwa a karamar hukumar Tsafe

- Biyo bayan lamarin, gwamnan jihar Zamfara ya ce gwamnatinsa za ta samar da hukuncin kisa a kan masu tukin ganganci

Magoya bayan gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) su goma sha biyar sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota a jihar.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa hatsarin ya afku ne bayan magoya bayan PDP sun yi masa maraba da zuwa a karamar hukumar Tsafe.

Legit.ng ta tattaro cewa hatsarin ya faru ne a ranar Laraba, 26 ga watan Agusta, a hanyar Sokoto-Gusau.

Kakakin gwamnan, Zailani Bappa, ya ce mutanen da hatsarin ya cika da su sun kasance magoya bayan gwamnan a karamar hukumar wadanda suka taru domin yi masa maraba a hanyarsa ta dawowa daga Abuja a yammacin ranar Laraba.

Atiku ya yi martani yayinda hatsarin mota ya kashe magoya bayan PDP 15 a Zamfara
Atiku ya yi martani yayinda hatsarin mota ya kashe magoya bayan PDP 15 a Zamfara Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Da yake magana kan hatsarin a ranar Asabar, 29 ga watan Agusta, Gwamna Matawalle ya ce gwamnatinsa za ta fara yanke hukuncin kisa ga direbobi masu tukin ganganci.

KU KARANTA KUMA: Zamfara za ta fara yankewa masu tukin ganganci hukuncin kisa bayan mutuwar wasu magoya bayan gwamnan su 15

Wannan doka zai tabbatar da tilastawa direbobi masu tukin ganganci biyan diya kan kowani raid a aka rasa, gwamnan Zamfara ya kara da cewa.

Da yake martani kan ci gaban, tsohon mataimakin Shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya yi ta’aziyya ga gwamnatin jihar Zamfara da iyalan wadanda lamarin ya cika da su.

“Tunanina da addu’o’ina na tare da iyalai da abokan mutum 18, wadanda suka rasa ransu a hatsarin mota yayinda suke tarban Gwamna @Bellomatawalle1, a iyakar Zamfara da Katsina.

“A madadin iyalaina, ina mika ta’aziyya ga iyalan wadanda abun ya cika da su, Gwamna Matawalle da gwamnati da mutanen jihar Zamfara,” Atiku ya wallafa a shafinsa na twitter.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel