‘Dan wasa Messi ya ki zuwa wasa bayan ya rubuta takardar barin kulob
Shahararren ‘dan kwallon Duniya, Lionel Messi ya sanar da kungiyarsa ta Barcelona cewa ba zai fito aiki a yau Ranar Laraba ba.
Sabon darektan wasannin da kungiyar Barcelona ta nada, Ramon Planes ya bayyana matsayar ‘dan wasan a ranar 26 ga watan Agusta, 2020.
Ramon Planes ya ke cewa “Messi ya fada mana ba zai fito wasa ba.”
Planes ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke kaddamar da sabon ‘dan wasan gaban da Barcelona ta saya, Joao Trincao.
“Duk wata tattaunawa da za ayi za ta zama tsakanin bangarori biyu (kungiyar da ‘dan wasan), Saboda girmamawa, ba za mu bayyana tattaunawarmu ba.”
Darektan kungiyar ya ce su na bakin kokarinsu na ganin sun yi sulhu da Lionel Messi wanda ya bukaci ya bar kulob din bayan shekaru kusan 15.
A sakamakon wulakancin da Bayern Munich ta yi wa Barcelona ne aka kori Koci Quique Setien da Eric Abidal wanda aka maye gurbinsa da Ramos Planes.
KU KARANTA: Kungiyoyin da su ke da kudin da za su iya raba Messi da Barcelona
Barcelona ta ce ba ta da niyyar barin Messi ya tashi, za ta yi kokarin ganin cewa ya cigaba da taka leda a kungiyar da ya ke yi wa wasa tun shekarar 2004.
“Mu na yi wa Messi kallon ‘dan wasan Barcelona.”
“A yau Trincao ya zo, kuma mu na sa rai tauraruwarsa za ta haska tare da Messi.” Inji Planes.
“Ba sau daya ko biyu ba, Barcelona ta na dawowa da karfinta. Burinmu shi ne mu gina kungiya a karkashin gwarzon ‘dan wasan Duniya.” A cewar Planes.
Darektan wasannin ya kara da cewa: “Dole a ga darajar Messi saboda abin da ya yi.”
"Ba mu tunanin saida shi, zaman Messi a Barcelona ya kawowa magoya baya farin ciki. Mu na kokarin ganin ya zauna." Planes ya fadawa AFP.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng