Ize iyamu: Ni ba yaron Oshiomole bane, shi ne karan farauta na

Ize iyamu: Ni ba yaron Oshiomole bane, shi ne karan farauta na

Dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Edo, Osagie Ize-Iyamu ya ce Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam’iyyar na kasa ba ubangidansa bane.

Da yake zantawa da Arise TV a ranar Lahadi, Ize-Iyam ya ce shi ya janyewa Oshiomhole a 2007 domin tsohon shugaban na APC ya samu cimma burinsa na zama gwamnan Edo.

Ize-Iyamu ya ce shi ba sabo bane a harkar sabanin Godwin Obaseki, gwamnan jihar mai mulki, wanda ke bukatar wani ya koya masa yadda ake murza kambun.

"A 2007, domin ganin ya zama gwamna...mutanena suka bukaci da na zama gwamna amma na janye masa saboda yankinsa bai taba samun gwamna ba, ya fito ne daga yankin Edo ta arewam,” in ji shi.

“Daga inda na fito, Edo ta kudu maso yamma mun taba samun gwamna. Kawai na duba hakan ne domin a samu daidaito, yana da kyau mutum ya kafa tarihi. Tabbass, ya yi wa APC kokari sosai a matsayin shugaba kuma na fadi, kun san yana da kyau.

Ize iyamu: Ni ba yaron Oshiomole bane, shi ne karan farauta na
Ize iyamu: Ni ba yaron Oshiomole bane, shi ne karan farauta na
Asali: Facebook

“Don haka yaya mutum kamar ni zai bayyana shi a matsayin ubangida ko nace Oshiomhole ne ubangidana... kan wani dalili? Mun samu tarihi na sabani, mun saba sannan mun dawo tare, don haka abunda kuke gani kawai mutunci ne.

“Eh, kuna iya cewa shi ya kawo Obaseki amma ai Obaseki sabon shiga ne, ba za ku iya kwatanta shi da niba. Na riki mataimakin shugaban ACN na kasa; ina daya daga cikin wadanda suka shirya kundin tsarin APC. Bai yi rayuwa a nan ba duk da cewar a na aka haife shi, daga Lagas ya zo, don haka yana bukatar ubangida, yana bukatar wani da zai horar da shi sannan ya tayar dashi.

“Amma ni, kuna maganar babba ne, akwai mutane da dama da na rena. A duk fadin jihar, suna kallona a matsayin shugaba.

KU KARANTA KUMA: Dubban masoya sun yi tururuwar fitowa a Kaduna domin tarban tsohon Sarkin Kano, Sanusi

“Ni ina da mutunta manyana. Ina ganin mutunccin wadanda suka yi nasara a fannoni daban-daban, hatta na kasa dani kuma zancn gaskiya shine ina mutunta mutane ba zan taba kaskantar da wani ba saboda na kasance gwamna. Don haka idan ana maganar ubangida, ku janye shi.

“Oshiomhole na yi mun aiki ne, yana mun kamfen ne saboda shima yana son jam’iyyarsa ta lashe zaben Edo kuma ba za ku iya karbe hakan daga gareshi ba.”

Dan takarar gwamnan ya yarda cewa mutane sun tsorata da alakar da ke tsakaninsa da Oshiomhole.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta

Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel