Kamar Jigawa, lauyoyin Bauchi sun yi uwar kungiya bore saboda janye gayyatar El-Rufa'i

Kamar Jigawa, lauyoyin Bauchi sun yi uwar kungiya bore saboda janye gayyatar El-Rufa'i

Kungiyar Lauyoyin Najeriya, shiyar Jihar Bauchi, ta bi sahun takwararta ta jihar Jigawa wajen fasa halartar taron gangamin yanar gizon da uwar kungiyar ta shirya sakamakon janye gayyatar da ta yiwa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

Hakan ya bayyana takardar da kungiyar NBA Bauchi, ta saki dauke da rattafa hanun shugabanta, Abubakar AbdulHamid da Sakatare Shamsudeen Magaji, ranar Juma'a 21 ga Agusta, 2020.

Kungiyar ta Bauchi ta bayyana cewa uwar kungiya ta sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya da ya bada daman kyautatawa mutum zato har sai an tabbatar da laifi a kansa.

Ta yi kira da uwar kungiya ta dawo da El Rufa'i ko ta kauracewa taron gangamin da aka shirya gudanarwa makon gobe.

"Idan uwar kungiya bata janye daga shawararta ba, sashenmu ta yanke shawarar kauracewa taron gangamin da aka shirya shekarar nan," Jawabin yace

Kamar Jigawa, lauyoyin Bauchi sun yi uwar kungiya bore saboda janye gayyatar El-Rufa'i
Kamar Jigawa, lauyoyin Bauchi sun yi uwar kungiya bore saboda janye gayyatar El-Rufa'i
Asali: Twitter

KU KARANTA: Daga karshe, El-Rufa'i ya amince da bude Masallatan khamus-salawaati a Kaduna

Kamar Jigawa, lauyoyin Bauchi sun yi uwar kungiya bore saboda janye gayyatar El-Rufa'i
Kamar Jigawa, lauyoyin Bauchi sun yi uwar kungiya bore saboda janye gayyatar El-Rufa'i
Asali: Twitter

A jiya, Kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) ta janye gayyatar da ta yi wa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, zuwa wurin babban taronta bayan wasu daga cikin mambobin kungiyar sun nuna rashin amincewarsu.

NBA, wacce ta saka sunan El-Rufa'i a cikin manyan baki da za su gabatar jawabi a wurin taron, ta sanar da cewa ta janye gayyatar da ta yi masa a shafinta na Tuwita a ranar Alhamis.

"Shugabannin kungiyar NBA sun gana tare da yanke shawarar janye gayyatar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, zuwa wurin babban taronta na shekarar 2020 kuma za a sanar da gwamnan wannan shawara ta hannun kwamitin tsare-tsare," a cewar sanarwar.

Kimanin mutane 3,150 ne suka rattaba hannu a kan takardar nuna rashin amincewa da gayyatar El-Rufa'i zuwa wurin taron NBA wacce wani lauya, Usani Odum, ya rubuta domin yin korafi a kan gayyatar gwamnan.

A wata takarda daban da Farfesa Koyinsola Ajayi, shugaban kwamitin tsare-tsare na taron NBA, ya fitar a kan neman a janye gayyatar El-Rufa'i, ya bayyana cewa wasu lauyoyi sun bayyana cewa sam gwamnan ba zai yi magana a wurin taron ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Asali: Legit.ng

Online view pixel