Kotu ta yankewa Malamin makaranta hukuncin watanni 28 a Kurkuku kan laifin satar N28,000

Kotu ta yankewa Malamin makaranta hukuncin watanni 28 a Kurkuku kan laifin satar N28,000

Wata babbar kotu dake zamanta a Kasuwan Nama a Jos ranar Talata ta yankewa Malamin makaranta, Thomas Joshua, hukuncin watanni 28 a gidan yari kan laifin satan N28,000.

Alkali mai shari'a, Malam Lawal Suleiman, ya yanke hukuncin ne bayan Malamin ya amince da laifin da ake masa na sata, The Punch ta ruwaito.

Yayin yanke hukuncin kan laifin farko, Alkalin, ya bada daman zabin biyan taran N10,000 kan kowanne ko ya kwana a gidan yari.

Ya umurci Malamin makarantan ya kara biyan wanda ya kawo kara, Mr Ibrahim Saidu, N10,000.

Ya ce wannan hukunci zai zama izina ga dukkan wadanda ke tunanin aikata irin wannan laifi na sata.

Gabanin haka, lauyan hukumar yan sanda, Ibrahim Gokwat, ya bayyanawa kotu cewa Saidu ya kawo karan Thomas Joshua ofishin yan sandan Mista Ali ne ranar 16 ga Agusta, 2020.

Gokwat ya ce, Saidu ya baiwa Thomas Joshua ajiya wayar Salula amma sai ya cire layin wayar kuma ya kwashe kudi N28,000 daga asusun bankin Saidu ba tare da izininshi ba.

Lauyan ya ce wannan laifi ya sabawa sashe 297 da 272 na dokar Penal Code na jihar Plateau.

KU KARANTA: 'Yan APC 5,000 sun koma PDP a Edo, sun mara wa Obaseki baya

Kotu ta yankewa malamin makaranta hukuncin shekaru 2 a kurkuku kan satan N28,000
Kotu ta yankewa malamin makaranta hukuncin shekaru 2 a kurkuku kan satan N28,000
Asali: Depositphotos

Wata babbar kotun Ado Ekiti, jihar Ekiti ta yanke wa wani matashi mai shekaru 26 wanda aka ambata da suna Dele Ojo hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon kisan kai da yayi.

Mai shari’a Abiodun Adesodun ya bayyana cewa ya zartar da hukuncin ne sakamakon hujojjin da aka gabatar a gaban kotun wanda suka tabbatar da cewar Dele ya aikata laifin da ake tuhumarsa a kai a ranar 13 ga watan Satumban 2018.

Mai gonar doyan da mai laifin ya je sata a gonarsa ya dade yana fakon barawon da ke girbe masa doya domin kusan kullum idan ya garzaya gonar sai ya iske an yi masa barna.

A ranar da asirin Dele ya tonu sai aka kamashi yana hakar doyan yana dankara wa a wani katon buhu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel